Kungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FWF) ta rubuta wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya, tana neman a gaggauta sake duba albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 70,000 zuwa Naira 300,000.
A cikin wasikar mai kwanan wata 2 ga Satumba, 2026, wadda mai kula da kungiyar ta kasa, Andrew Emelieze, da Babban Sakataren kungiyar, Ogundele Ayodele, suka sanya wa hannu, an bukaci Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai su ɗauki matakin da ya dace, ta hannun Magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya.
Shugaba Tinubu, Alkalin Alkalai na Nijeriya da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ma na cikin wadanda aka aikawa wasikar.
Kungiyar ta kuma nemi a sanya albashin ma’aikatan da ke mataki na 17 zuwa Naira miliyan 1.5, tana mai cewa tsarin albashin da ake amfani da shi yanzu bai dace da yanayin tattalin arzikin da ma’aikatan gwamnatin tarayya ke fuskanta ba.A cikin wasikar, ma’aikatan sun ce: “Muna kira da a yi adalci tare da gaggauta sake duba albashi yanzu, a kara mafi karancin albashin tarayya zuwa Naira 300,000, sannan a sanya mafi girman albashi na Naira miliyan 1.5 ga ma’aikatan dake mataki na 17.”
FWF ta ce bukatar ta samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin rashin cikakken aiwatar da sabon mafi karancin albashin Naira 70,000 da aka amince da shi a shekarar 2024.
Kungiyar ta yi zargin cewa ma’aikatan gwamnatin tarayya ba su samu cikakken karin albashin da ya kamata ba, biyo bayan karin mafi karancin albashi, da kuma wasu alawus-alawus da ke da alaka da shi.
Ta ce, “Zai ba ku mamaki ku ji cewa Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da sabon mafi karancin albashin kasa gaba daya ba tun daga watan Yulin 2024. Mun dade muna fafutukar ganin an aiwatar da cikakken karin albashin da ya kamata biyo bayan sabon mafi karancin albashin.”
A cewar ma’aikatan, sake duba tsarin albashin da aka yi a shekarar 2024 ya kara mafi karancin albashi daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000, amma hakan ya haifar da karin Naira 40,000 kacal ga kowane mataki a cikin ma’aikatan gwamnatin tarayya.














