A yayin zama na 63 na majalisar kare hakkin bil’adama ta MDD ko UNHRC, wanda ya gudana a jiya Litinin, an amince da kuduri mai taken “Ingiza samar da damar cin gajiyar hakkin bil’adama ga kowa” wanda kasar Sin ta gabatar a madadin kasashe 47.
Cikin jawabinsa na gabatarwa, jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Jia Guide, ya ce gina yanayi na kyakkyawar dama, muhimmin jigo ne na kiyaye ikon dukkanin rukunonin jama’a, ta yadda za su iya cin gajiyar bai daya mai gamsarwa a harkokin zamantakewa, tare da morewa cikakkun hakkokin bil’adama.
A nasu tsokacin kuwa, wakilan kasashen Cuba da Masar, cikin wadanda suka bayyana goyon bayan kudurin, sun jinjinawa kasar Sin bisa aiki tukuru da ta yi wajen ingiza jigon “Samar da dama ga kowa”, tare da dorawa kan inda aka tsaya dangane da batun samar da dama ga kowa.
Wakilan sun yi imanin cewa, kudurin na kira da a samar da tallafin kwarewa ga kasashe masu tasowa, da ingiza hadin gwiwar kasa da kasa a fannoni masu nasaba da batun, bisa bukatun kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)














