Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kafa wani Sashen Fasahar Basirar Ɗan’adam (AI) na musamman a karkashin Sashen Fasahar Sadarwa da Kwamfuta (ICT), domin kara karfafa hanyoyin gano kura-kurai da dakile yada labaran karya gabanin babban zaben 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton halin da shirye-shiryen hukumar ke ciki na zaben 2027, a wani taron manema labarai na kasa da taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Amupitan ya ce tuni hukumar ta shigar da kayan aikin tantancewa da AI ke sarrafawa cikin tsarin tantance sakamakon zabe.
Ya bayyana cewa za a gudanar da amfani da fasahar ne karkashin wani tsarin kula da AI mai ginshikai guda biyar, tare da tabbatar da cewa mutane za su ci gaba da sa ido kan dukkan matakan amfani da fasahar.
Ya kara da cewa INEC na kammala tsara manufarta kan yadda za a tafiyar da amfani da AI, domin tabbatar da amfani da fasahar cikin tsari da rikon amana.














