ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Aka Ce Kasar Sin Ta Ceci Tattalin Arzikin Duniya?

by Sulaiman
2 months ago
Sin

A farkon rabin shekarar bana, sakamakon yakin da ya barke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, farashin mai na duniya ya yi tashin gwauron zabi, kuma matsalar makamashi ta shafi kasashe da dama, ciki har da dimbin kasashen Afirka. A ranar 31 ga Maris, gwamnatin Zambiya ta sanar da kafa dokar ta baci sakamakon matsalar samar da man fetur a kasar. Masanin ilimin makamashi na kasar, Johnstone Chikwanda, ya ce: “Muna fuskantar babbar barazana ta fannin tsaron makamashi, wadda ba Zambia kadai ta shafa ba, har da kimanin kashi 75% na sauran kasashen Afirka.”

Matsalar makamashi ta kan haifar da mummunan tasiri ga bunkasar tattalin arzikin duniya, musamman idan mun yi la’akari da matsalolin makamashi sau uku da aka fuskanta a karni na 20. Abin lura shi ne, a wannan karo, wasu kafofin yada labarai irin su Wall Street Journal na Amurka da Le Figaro na Faransa sun bayyana ra’ayin cewa: a lokacin yakin Amurka da Isra’ila da Iran, kasar Sin ba ta fafata da sauran kasashen duniya wajen sayen mai ba, kuma hakan ya taimaka wajen daidaita farashin mai a duniya, tare da ceton tattalin arzikin duniya a karo na biyu. (Karo na farko shi ne bayan rikicin kudi na duniya a shekara ta 2008, lokacin da kasar Sin ta yalwata yawan bukatun cikin gida, ta tallafa wa bukatun duniya gaba daya, wanda hakan ya taimaka wa tattalin arzikin duniya fita daga kangin koma baya.)

Me ya sa jaridun suka fadi haka?

ADVERTISEMENT

Lallai, tun bayan barkewar yakin Amurka da Isra’ila da Iran, mashigar tekun Hormuz, wacce take tamkar “makogwaron” jigilar makamashi a duniya, ta gamu da cikas sosai. A kowace rana, ana jigilar mai kusan ganga miliyan 20 ta mashigin Hormuz, wanda ya kai kashi 1/5 na man da ake jigilar a duniya. Idan mashigar ta gamu da cikas, damuwa da fargaba zai sa kasa da kasa su yi kokarin sayen mai daga kasuwannin duniya, wanda hakan zai haifar da hauhawar farashin mai. Duk da haka, kasar Sin, wacce take kan gaba wajen shigo da mai a duniya, ba ta shiga cikin kasashen da ke takarar sayen mai ba, a maimakon haka ta rage sayen mai na dan gajeren lokaci. A watan Mayu, man da kasar ta shigo da shi ya ragu zuwa ganga 780,000 a kowace rana, wanda ya ragu da kashi 29% idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata, kuma shi ne mai mafi karanci da ta shigo da shi tun bayan shekara ta 2018. Rage sayen mai da ya kai sama da ganga miliyan uku a kowace rana, ya sassauta damuwar kasashen da ke kokarin sayen mai a kasuwannin duniya, wanda hakan ya taimaka wajen saukar da farashin mai. Ga Afirka, wannan yana nufin an sassauta matsalar hauhawar farashin kayayyaki da ake shigarwa daga waje. Wannan shi ne dalilin da ya sa jaridun kasashe daban daban suka dauki kasar Sin a matsayin muhimmin karfi mai tallafawa kokarin daidaita rikicin mai a duniya.

Amma me ya sa kasar Sin ta iya rage sayen mai a maimakon kara sayowa a yayin rikicin? To, dalili shi ne canji mai zurfi da ta samu a tsarin makamashinta. A baya, kasar Sin ta kasance tamkar “injin” da ke kara yawan bukatun mai a duniya. Bisa ga Littafin Kididdigar Makamashi ta Duniya, daga shekara ta 2005 zuwa 2024, yawan man da kasar Sin ta yi amfani da shi ya ninka fiye da sau biyu, wanda ya kai sama da rabin yawan karuwar bukatun mai na duniya a wadannan shekaru. Amma a shekara ta 2024, an samu sauyi, inda yawan man da kasar ta yi amfani da shi a fannin sufuri ya ragu, kuma a wannan shekarar, sakamakon karuwar motocin lantarki da ake amfani da su a kasar, yawan man da ake amfani da shi a kowace rana ya ragu da ganga 430,000. Wannan canji bai faru ba zato ba tsammani ba. Tun bayan da kasar Sin ta zama kasar da yawan man da take shigo da shi ya zarce wanda take fitarwa zuwa ketare, kuma ta dogara ga kasashen ketare wajen shigo da kaso 70% na mai da take bukata, a sannan kasar ta san cewa, bai kamata a damka makomar makamashi a hannun wasu ba. A watan Mayu na shekara ta 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara wani kamfanin kera motoci, inda ya ce: “Raya motoci masu amfani da sabbin makamashi ita ce hanya tilo da kasar Sin za ta bi don sauyawa daga kasa mai yawan motoci zuwa kasa mai karfin hada da amfani da motoci.” Bayan shekaru goma sha biyu, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da aka samar a kasar ya karu daga 78,500 a shekara zuwa sama da miliyan 16, wanda ya ninka har sau 200. Ya zuwa karshen watan Mayu na shekara ta 2026, karfin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya kai kilowatt biliyan 4.01, kuma karfinta na samar da lantarki bisa makamashin zamani ya kai kashi 62%. Kasar Sin ta gina tsarin samar da makamashin da ake sabuntawa mafi girma kuma mafi saurin bunkasa a duniya, wannan kuma ya baiwa kasar Sin karfin tinkarar rikicin.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Wannan ya kuma ba wa Afirka muhimmin darasi. Afirka ita ce nahiya mafi arzikin albarkatun hasken rana, iska da ruwa a duniya, amma har yanzu akwai kusan mutane miliyan 600 da suke fuskantar matsalar rashin wutar lantarki. A shekarun baya-bayan nan, kamfanonin Sin a kasashen Najeriya, Afirka ta Kudu, Kenya, Habasha da sauran kasashen Afirka sun gina ayyukan samar da wutar lantarki ta ruwa, hasken rana da iska, wadanda ke taimakawa wajen rage dogaro ga samar da wutar lantarki daga man dizal, kuma yana baiwa kasashen Afirka damar shiga zamanin makamashi mai tsafta cikin farashi mai rahusa.

Tsaron makamashi yana shafar rayuwar iyalai da injunan masana’antu da kuma makomar kasashe. Kasar Sin bisa yadda ta gyara tsarin makamashinta, ta ba da amsarta, wato ya zama dole a tabbatar da ci gaban kasa bisa makamashin da ake sabuntawa, kuma Sin da Afirka suna iya hadin gwiwa a fannin, tare da cin gajiyarsa.

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ta’addanci

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Takwas A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.