ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Kaduna

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yabawa Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) bisa ƙaddamar da shirin Forest Guards, tana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki wajen magance matsalar rashin tsaro a dazuka da yankunan karkara. Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da ya karɓi wata babbar tawaga daga ONSA ƙarƙashin jagorancin Daraktan Harkokin Tsaro, Manjo Janar HI Mabeokwu, a Gidan Gwamnatin Kaduna.

Tawagar ta kai ziyarar ne domin tantance ci gaban horon sama da masu gadin daji 1,000 masu ɗauke da makamai, waɗanda ake shiryawa domin tura su zuwa yankunan da ake fama da matsalar tsaro a faɗin jihar Kaduna. Gwamna Uba Sani ya ce wannan shiri na nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da jin daɗin masu horo da masu horas da su.

A nata ɓangaren, tawagar ONSA ta nuna gamsuwa da yadda horon ke gudana, tana mai cewa an tsara shirin cikin tsari kuma an samar da isassun kayan aiki da wuraren gudanar da horon. Har ila yau, ta yabawa gwamnatin Kaduna bisa tallafin jin daɗi da take bai wa masu horo da masu horas da su tun bayan fara shirin.

ADVERTISEMENT

Jami’an da ke kula da shirin sun bayyana cewa masu horon sun kammala kusan kashi 60 cikin 100 na tsarin horaswar, wanda ya haɗa da koyon amfani da makamai, da dabarun gudanar da ayyukan tsaro da sauran ƙwarewar da ake buƙata wajen tsaron dazuka. Tawagar tantancewar ta ƙunshi wakilai daga Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), da Hukumar DSS, da kula da Gandun Daji, da Rundunar ‘Yansandan da kuma Sojojin Nijeriya. Shirin na daga cikin Presidential Forest Guards Initiative, wanda ke da nufin ƙwato dazukan da ‘yan ta’adda, da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke amfani da su a matsayin mafaka, inda ake sa ran masu gadin dajin za su yi aiki tare da hukumomin tsaro wajen tattara bayanan sirri da sintiri a yankunan dazuka.

Kaduna
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi
Tsaro

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026
Next Post
Me Ya Sa Aka Ce Kasar Sin Ta Ceci Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Aka Ce Kasar Sin Ta Ceci Tattalin Arzikin Duniya?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.