ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

DSS Ta Kama ‘Yar Jarida Zainab Sodiq Kan Zargin Mallakar Drone Ba Tare da Cikakkun Takardu ba

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Zainab

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

DSS ta tabbatar da kama Zainab Sodiq, ‘yar jaridar da ke bibiyar ayyukan ɗan siyasa Omoyele Sowore, bisa zargin mallakar jirgi maras matuki (drone) ba tare da takardun da doka ta tanada ba. A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Sadarwa ta DSS, Favour Dozie, ya fitar ranar Alhamis, ya ce jami’an DSS tare da na Tsaron Sufurin Jiragen Sama (AVSEC) sun tare ta ne a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar 6 ga Yuli.

Sanarwar ta ce an same ta da jirgin sama mara matuƙi (UAV) yayin da take shirin tafiya Abuja, amma ba ta da Takardar Izinin Amfani (End User Certificate – EUC) da ake buƙata. DSS ta ce, bayan an tambaye ta, ta amsa cewa ba ta mallaki takardun da suka dace ba. Duk da haka, an ba ta damar ci gaba da tafiyarta zuwa Abuja saboda wani muhimmin alƙawari da take da shi, tare da umartar ta da ta kai kanta shalkwatar DSS a ranar 8 ga Yuli domin ci gaba da bincike.

Hukumar ta bayyana cewa binciken na gudana ne bisa ƙa’idojin da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA) ya kafa, waɗanda suka tanadi sharudda kan mallaka da amfani da jiragen sama marasa matuƙa. A cewar DSS, ƙa’idojin sun bai wa hukumar ikon ƙwacewa da hukunta duk wanda aka samu yana amfani da irin waɗannan jirage ba tare da amincewar hukuma ba, saboda matsalolin tsaro da suka haɗa da take sirri da kuma barazanar tsaron rayuka.

ADVERTISEMENT

Sai dai da yake mayar da martani a shafinsa na X, Omoyele Sowore ya yi zargin cewa an tsare Zainab Sodiq ne saboda aikinta na jarida. Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin tsoratar da masu sukarsa, yana mai cewa kama ‘yar jaridar ba zai dakile aikinsu ba. Sai dai DSS ta dage cewa matakin da ta ɗauka ya yi daidai da dokokin tsaro da ke kula da amfani da jiragen sama marasa matuƙa a Najeriya.

Zainab
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Zainab

TCN Ta Kammala Gyaran Layin Wutar Lantarkin Zaria–Funtua 132kV

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.