Manoman shinkafa a ƙananan hukumomin Yauri, Ngaski da Shanga a Jihar Kebbi sun nemi taimakon gwamnati bayan ambaliyar kogin Neja ta lalata musu amfanin gona.
Manoman sun ce sun yi asarar shinkafa ta miliyoyin Naira, inda yawancinsu suka kashe dukiya mai yawa da fatan samun girbi mai kyau, amma yanzu babu abin da ya rage musu.
- Dole Ne A Nace Kan Manufar Sin Daya Tak Don Kiyaye Zaman Lafiya A Mashigin Taiwan
- Tinubu Ya Isa Japan Don Halartar Taron TICAD9
Ɗaya daga cikin manoman da abin ya shafa, Shuaibu Gidanbindigawa, ya bayyana lamarin a matsayin abin mamaki da bai taɓa ganin irinsa ba.
“Da farko ruwa daga kogin Neja ya shafe gonakinmu, daga bisani ruwan sama ya gama da sauran abin da ya rage. Mun yi asara gaba ɗaya. Manoma a Shanga, Yauri da Ngaski sun shiga tsaka mai wuya. Sai dai mu roƙi Allah Ya kawo mana sauƙi,” in ji shi.
Ya yi kira ga shugabannin siyasa da su ɗauki matakin gaggawa, inda ya bayyana cewa ba wai kawai zuwa yi musu jaje suke buƙata ba.
“Wasu manoma da suke girbe buhun shinkafa fiye da 100 yanzu babu abin da ya rage musu. Ruwan ya lalata komai. Abin da muke buƙata taimako ne, ba wai ziyarar jaje kawai ba. Da dama daga cikinmu mun zuba dukiyarmu a cikin waɗannan gonaki. Gwamna, jama’arka na cikin matsanancin hali,” in ji shi.
Yauri, Ngaski da Shanga na daga cikin manyan wuraren da ake noma shinkafa a Jihar Kebbi.
Wannan ambaliya ta jefa rayuwar manoman da kuma samar da abinci cikin hatsari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp