ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

by Sadiq
48 minutes ago

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar mashaƙo a Jihar Filato ya ƙaru zuwa 27, yayin da adadin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ya kai 303.

Likitan kula da cututtuka masu yaɗuwa na jihar, Dokta Maren Damulak ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Jos.

Ya ce kashi 99 cikin 100 na waɗanda ake zargin sun kamu da cutar suna Jos ta Arewa

ADVERTISEMENT

Damulak ya ce yawancin mutanen da cutar ta kama ba su yi allurar rigakafin cutar mashaƙo ba.

Ya kuma ce yara na daga cikin waɗanda cutar ta fi shafa, yayin da al’ummar Rikkos da ke Jos ta Arewa na daga cikin wuraren da cutar ta fi ƙamari.

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

A makon da ya gabata, gwamnatin jihar Filato ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu, bayan gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Bassa da Wase.

Gwamnatin ta ce matakin na da nufin rage yaɗuwar cutar tsakanin ɗalibai da ma’aikatan makarantu, yayin da hukumomin lafiya ke sa ido da ɗaukar sauran matakan daƙile cutar.

Wasu daga cikin marasa lafiyar na samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) da Asibitin Kwararru na Jihar Filato, inda aka tanadi wuraren killace waɗanda suka kamu da cutar.

Haka kuma, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ta ƙara samar da babura da sauran kayan aiki domin taimakawa wajen gano mutanen da suka yi hulɗa da masu cutar, sa ido da wayar da kan al’umma.

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayar da umarnin gaggauta samar da magunguna da sauran kayan aikin lafiya a asibitoci domin taimakawa wajen shawo kan cutar.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, John Kyohroh Christopher, ya yi kira ga mazauna yankin da su kula da tsaftar jiki da muhalli domin rage yaɗuwar cutar.

MASU ALAKA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.