ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

by Sadiq
52 minutes ago

Ambaliyar ruwa ta tafi da wasu yara biyu ‘yan shekara 13 a Abuja da Jihar Abia bayan ruwan sama mai ƙarfi.

A Gwagwalada da ke Abuja, Alhassan Jamil, ɗalibin ƙaramar sakandare, ambaliyar ruwa ta tafi da shi a safiyar ranar Laraba yayin da yake kan hanyar zuwa makaranta tare da mahaifinsa a kan babur.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na safe a kusa da wani gidan mai da ke hanyar Old Kutunku-Market.

ADVERTISEMENT

An ce yaron ya faɗa cikin wata magudanar ruwa da ruwa ya cika ta maƙil yayin da suke ƙoƙarin ketare hanya.

Mahaifinsa ya yi ƙoƙarin ceto shi, amma ƙarfin ruwan ya yi awon gaba da yaron.

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

An samo masunta da wasu mazauna yankin domin nemo shi, amma har zuwa lokacin da haɗa wannan rahoto, ba a gano gawarsa ba.

A Umuahia ta Jihar Abia kuma, wata yarinya ‘yar shekara 13, Adekunle Emanuella Ige, ambaliyar ruwa ta rutsa da ita a yammacin ranar Litinin.

Rahotanni sun ce yarinyar ta faɗa cikin wata babbar magudanar ruwa yayin da take dawowa gida lokacin ruwan sama mai ƙarfi.

Ruwan ya shafe magudanar, lamarin da ya sa ba a iya bambance magudanar da hanyar da ake bi.

Mazauna yankin sun fara neman yarinyar har zuwa ranar Talata, amma ba a samu nasarar gano ta ba.

Mahaifiyarta ta roƙi mazauna yankin da hukumomin gwamnati da su taimaka wajen nemo ‘yarta.

Lamarin sun haifar da tashin hankali kan hatsarin ambaliyar ruwa, musamman a wuraren da magudanan ruwa ba su da zurfi.

A Abuja, hukumomi sun sha gargaɗin mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ke yawan shafa da su ɗauki matakan kariya.

Rashin isassun magudanan ruwa, toshewar hanyoyi da gine-gine a kusa da hanyoyin ruwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara haddasa ambaliyar.

MASU ALAKA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.