Ƙungiyar Christian Solidarity Worldwide (CSW) ta Nijeriya ta ce aƙalla masu ibada 17 da ’yan bindiga suka sace yayin hare-haren da suka kai wasu majami’u a Jihar Kaduna sun mutu a hannun waɗanda suka sace su, yayin da aka sako wasu mutane takwas.
Babban Daraktan ƙungiyar, Fasto Dr Yunusa Nmadu ne, ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a Cocin ECWA Goodnews da ke Kaduna, domin bikin Ranar Addu’a ta Duniya da Kiristanci suka gudanar.
Ya ce ’yan bindiga sun sace masu ibada 37 daga majami’u uku a garin Ariko, da ke Ƙaramar Hukumar Kachia, a ranar 5 ga watan Afrilu, 2026.
A cewarsa, mutum 12 sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen a lokuta daban-daban, 17 sun mutu a tsare, yayin da aka sako sauran mutum takwas bayan shafe watanni biyar a hannunsu.
Nmadu ya kuma bayyana cewa an sace mutane 11 a ƙauyen Awon, da ke Kachia, ranar 20 ga watan Afrilu, 2026.
Ya ce mutum ɗaya ya tsere, shida sun mutu, yayin da huɗu ke hannun masu garkuwar.
Ya ƙara da cewa an taɓa sace masu ibada 177 daga majami’u uku a garin Kurmin Wali, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru, a ranar 18 ga watan Janairu, 2026.
Daga bisani, an sako su bayan shafe kwanaki 18 a hannun masu garkuwar.
Daraktan ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-hare, kashe-kashe da sace mutane ke ci gaba da faruwa a sassa daban-daban na Kaduna, lamarin da ya tilasta wa dubban mazauna yankunan barin gidajensu.
Ya kuma yi zargin cewa masu garkuwar na gallaza wa waɗanda suke tsare da su, musamman mata da yara, ta hanyar cin zarafinsu ta yi musu fyaɗe, hana su abinci da sauransu.
Nmadu ya yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin addinai da su ƙara himma wajen kare rayukan al’umma da kuma taimakawa wajen ceto mutanen da har yanzu suke tsare a hannun maharan.













