Mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng ya gana da kwamishinan kungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin ciniki tattalin arziki da tsaro Maros Sefcovic a jiya Juma’a a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda suka yi musayar ra’ayi kan karfafa alakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.
A jawabin da ya gabatar, He ya ce a ko da yaushe kasar Sin na ba da muhimmanci mai karfi kan bunkasa alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da kungiyar Tarayyar Turai, kuma a shirye take, ta yi aiki da EU domin aiwatar da muhimman batutuwan da shugabanin bangarorin biyu suka cimma matsaya a kai.
A nasa bangaren, Sefcovic ya ce kasar Sin babbar abokiyar huldar kungiyar Tarayyar Turai ce a harkokin tattalin arziki da ciniki, yana mai cewa EU a shirye take ta ci gaba da karfafa alakar cinikayya da zuba jari, tare da karfafa sadarwa domin hada hannu wajen bunkasa hadin gwiwa a tsakaninsu.
Sin da kungiyar EU sun amince su ci gaba da kyautata alakar cinikayya da tattalin arzikin tsakaninsu, domin daidaita tsarin yadda ya kamata, tare da sanya watan Maris din shekarar 2027 domin sake ganawa da juna, karkashin tsarin tuntuba kan tattalin arziki da ciniki, kamar yadda sanarwar da bangarorin biyu suka fitar a Jumma’a.
Wata sanarwa da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta wallafa, ta ce ministan kasuwanci na kasar Wang Wentao da kwamishinan harkokin kasuwanci, tattalin arziki da tsaro na EU Maros Sefcovic, su ne suka jagoranci ganawar da aka yi kan alakar ciniki da zuba jari tsakanin Sin da EU, wanda ya gudana a ranakun Alhamis da Jumma’a a birnin Beijing.
Ma’aikatar ta kara da cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai ma’ana, tare da amincewa kan wasu muhimman batutuwa, da kuma cimma matsaya kan wasu batutuwa 16 da suka shafi ciniki da zuba jari, daidaita tsarin fitar da kayayyaki, hakkokin mallakar fasaha da kuma sauye-sauye a Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO). (Suleiman Suleiman )














