Masu ababen hawa a Nijeriya za su iya sayen man fetur a farashi mai rahusa a gidajen man NNPC, bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage farashi na tsawon kwanaki 30.
Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele ne, ya sanar da wannan rangw farashin a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa rangwamen ya shafi gidajen man NNPC ne kaɗai.
Ga hanyoyi biyar da za a bi domin samun man a farashi mai rahusa:
1. Sauke manhajar NNPC Fuel App: Sauke manhajar NNPC Fuel App daga manhajar Google Play ko Apple App Store, sannan ka yi rajista.
Dole ne masu ababen hawa su yi amfani da manhajar domin sanin farashin.
2. Biyan kuɗi ta manhajar a gidan mai: Ragin farashin ya shafi kowace litar man fetur da aka saya ta manhajar a gidajen man NNPC. Haka kuma, manhajar na taimakawa wajen gano gidan mai mafi kusa.
NNPC ya bayyana cewa rangwamen ya shafi gidajen manta ne kawai, kuma ba a tilasta wa sauran ’yan kasuwa su rage farashinsu ba.
3. Sayar da man kafin ƙarshen 31 ga watan Oktoba: An fara yin ragin ne a ranar 1 ga watan Oktoba a matsayin wani ɓangare na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya.
Ragin zai ci gaba da wakana har zuwa ƙarshen watan Oktoba a gidajen man NNPC da ke faɗin ƙasar.
4. Masu motocin haya su yi rajista: Gwamnatin Tarayya ta bai wa masu ababen hawa na haya fifiko a cikin shirin.
Don haka, direbobin haya, ƙungiyoyin sufuri da masu motocin haya da su sauke manhajar tare da yin rajista domin cin gajiyar ragin farashin.
5. Duba farashin lita domin sanin adadin kuɗin da mutum zai biya: An rage Naira 66 a kan kowace litar man fetur.
Ana cire wannan kuɗi ne daga farashin da ake sayar da man fetur, maimakon sanya farashin a cikin ainahin kuɗin mai da ake sayarwa.
Misali, idan ana sayar da litar man fetur kan naira 1,370 a Abuja, wanda ya biya ta manhajar zai biya naira 1,304 a kan kowace lita.
A Legas kuwa, idan farashin lita ya kai Naira 1,350, mutum zai biya Naira 1,284 kan kowace lita.
NNPC ta jaddada cewa an samar da shirin ne domin rage wa ’yan Nijeriya tsadar fetur, ba wai don dawo da tallafin man fetur ba.














