A ranar 25 ga watan nan ne, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York na kasar Amurka, tare kuma da halartar babban taron tattaunawa na cika shekaru biyar da gabatar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya (GDI) da kasar Sin ta karbi bakuncinsa, da karanta sakon shugaba Xi Jinping na murnar taron.
A ganawarsa da Antonio Guterres, Han Zheng ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 55 da mayar wa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin halastacciyar kujerarta a MDD. A cikin shekaru 55 da suka gabata, har zuwa yanzu, Sin ta tsaya ga bin ra’ayin mu’amalar mabambantan sassa a duniya, da goya wa MDD baya wajen taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar a-zo-a-gani a matsayin wata babbar kasa, da himmatuwa wajen kara hada akidu da shawarwarinta da ajandar MDD, gami da samar wa duniya sabbin damarmaki bisa sabbin nasarorin da ta samu wajen zamanantar da kasa.
Antonio Guterres a nasa bangaren kuwa, gode wa kasar Sin ya yi saboda babban goyon-bayan da take bayarwa ga sha’anin MDD, inda ya ce, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba ga muhimmiyar ajandar MDD, tare da bayar da babbar gudummawa ga ci gaban duk duniya baki daya.
Har wa yau, a babban taron tattaunawa na cika shekaru biyar da gabatar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya (GDI), mataimakiyar babban sakataren MDD, Amina Mohammed, da firaministan kasar Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif, da mataimakin shugaban kasar Maldives, Hussain Mohamed Latheef, gami da mataimakin firaministan kasar Laos kuma ministan harkokin wajen kasar, Thongsavanh Phomvihane, sun gabatar da jawabai daya bayan daya, kuma manyan jami’ai daga kasashe sama da 30, da wakilai fiye da 300 daga kasashe sama da 60 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 20 su ma suka halarci taron.
Bangarori daban-daban sun yaba sosai da muhimmiyar rawar da shawarar raya ci gaban duk fadin duniya ta taka, tun bayan da aka gabatar da ita shekaru biyar da suka wuce har zuwa yanzu, musamman a fannonin da suka shafi samar da ci gaba mai dorewa ga sassan kasa da kasa, da taimaka wa aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030. (Murtala Zhang)














