Akwai wani ra’ayi da ya dade da yaduwa na cewa akwai hanya guda daya kacal ta samun zamanantarwa, wato bin hanyar kasashen yammacin duniya. A cewar wannan ra’ayi, duk kasar da ke son samun zamanantarwa, dole ne ta rungumi tsarin ci gaban kasashen yammacin duniya gaba daya.
Ba za a musanta cewa tsarin ci gaban zamanantarwa na kasashen yammacin duniya ya bada gudummawa mai muhimmanci ga bunkasa karfin samar da hajoji da kuma ci gaban wayewar kan bil’adama ba.
Sai dai kuma, matsalolin da suka samo asali daga wannan tsari, musamman yadda jari hujja ke zama jigon manufofin ci gaba da kuma rashin daidaiton ci gaba, sun bayyana a fili.
A lokuta da dama, muradun jari hujja suna gaban muradun jama’a, kana gibin ci gaba tsakanin yankuna da al’umma na ci gaba da fadada, kuma tarin dukiyar wasu ’yan kalilan na samuwa ne ta hanyar karanta jin dadi da walwalar mafi yawan jama’a.
A shekaru sama da dari na aikace-aikacen da Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta gudanar, ta rungumi wata muhimmiyar manufa wadda ta kauce wa abin da mutane da yawa suke ayyanawa a matsayin “amsar da ta dace” kawai. Wannan manufa ita ce, muradun jama’a na gaban komai. (Murtala Zhang)














