Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin na ci gaba da bin manufofi da ka’idojin kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a-kai-a-kai tare da bayar da cikakken goyon baya ga ayyukan MDD.
Wang, wanda har ila yau mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da Carolyn Rodrigues-Birkett, wakiliyar dindindin ta kasar Guyana a MDD kuma ‘yar takarar mukamin babban sakataren MDD na gaba, a birnin Beijing.
Ya bayyana cewa, kasar Sin za ta shiga cikin zaben babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na gaba cikin tsari na sauke nauyin da ke wuyanta da kuma tasiri mai kyau, tare da goyon bayan zabar sabon babban sakatare wanda zai mutunta kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna kwarewa ta musamman, da yin aiki cikin gaskiya da adalci, tare da gudanar da ayyukan da ke kansa cikin sadaukarwa, daidai da tanade-tanaden kundin tsarin majalisar ta dinkin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














