Wani dan yawon bude ido mai suna Urvie, daga Birtaniya wanda a baya-bayan nan ya kammala yawon shakatawa a kasar Sin, ya bayyana gamsuwa da abubuwan da ya gani, yana mai bayyana Sin a matsayin kasa mai kayatarwa.
A baya-bayan nan Urvie ya kammala yawon bude ido karo na uku a kasar Sin, inda a wannan karo ya ziyarci birane da suka hada da Xi’an da Lhasa, ya kuma bayyana fatansa na sake bin hanyar siliki ta kasa a shekara mai zuwa. Shi ma wani dan yawon bude ido daga Netherland mai suna Bahar, ya shirya shafe ‘yan makonni kadan a Sin, amma daga karshe ya shafe watanni shida a cikin kasar.
Kazalika, wasu kafofin sada zumunta na intanet, sun wallafa hamshakin dan kasuwar nan na Amurka, kuma mamallakin kamfanin Tesla Elon Musk, yana jinjinawa kasar Sin, tare da karfafa gwiwar dukkanin al’ummun kasa da kasa da su ziyarci kasar ta Sin, a wani mataki dake karfafa karsashin masu yawon bude ido na kasa da kasa ziyartar kasar Sin.
Jerin alkaluma sun fayyace hakan, sun kuma fitar da bayanai dalla-dalla. Cikinsu wata kididdiga ta nuna yadda a rabin farko na shekarar nan ta 2026, adadin baki miliyan 22.914 sun shigo kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 20.4 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata. Cikin wannan adadi, kaso 77.7% sun shigo Sin ne ba tare da bukatar biza ba, adadin da ya karu da kaso 30.6% idan an kwatanta da na shekarar bara. Yayin da ake kara inganta manufofi irinsu mayarwa baki masu ziyara kudaden haraji yayin da suke barin kasar, adadin baki ‘yan kasashen waje da suka mika bukatun karbar irin wannan nau’i na haraji a rabin farko na shekarar nan ya karu da kaso 366%.
To ko me ya sa baki masu ziyartar kasar Sin ke kara jimawa a cikin kasar tamkar ba sa son komawa gida? Daraktan cibiyar harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin Dai Bin, ya ce kasar Sin na da dadadden tarihi da yankuna masu matukar fadi, wadanda ke samarwa ‘yan yawon bude ido da abubuwa masu tarin yawa, ta yadda zai yi wuya baki masu yawon bude ido su iya fahimtar su baki daya a ziyarar farko.
A daga bangaren kuma, ci gaba da bunkasar ingancin rayuwa, da kara daga matsayin manufofi, da tsaro da daidaiton yanayin zamantakewa, da yanayin bude kofa da abota na al’ummun Sin, sun ci gaba da karfafa karbuwar kasar ga masu shigowa yawon bude ido. Don haka yawan ziyartar kasar a lokuta daban daban zai ba su damar zurfafa fahimta, da kallon kasar ta kyakkyawar mahanga, da game dukkanin sassan fahimtar kasar. (Saminu Alhassan)














