Bukukuwan baje koli da dama da aka yi a watan Satumba, ciki har da na cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin watau CIFIT da na cinikayyar hidimomi watau CIFTIS, sun ja hankalin shugabannin kamfanonin kasa da kasa.
Bayan kammala baje kolin kuma, wasu daga cikinsu ba su koma gida kai tsaye ko sun tafi yawon bude ido ba, maimakon haka, sai suka zarce zuwa masana’antun kasar Sin.
Baje koli na zaman wata gada ta hada Sin da kasashen waje, yayin da masana’antun Sin da tsarin samar da kayayyaki da yanayin ayyuka daban-daban ke zaman tubalin sauya jari zuwa riba.
Yadda shugabannin kamfanonin kasashen waje ke tururuwan zuwa masana’antun da ke gaba gaba a bangarorinsu, alamu da ke nuna cewa kamfanonin kasashen waje na cin gajiyar damarmakin da Sin ta samar.
Shugabar kamfanin GSMA, Sihan Bo Chen ta ce “kasar Sin wuri ne mai kyau na gwajin aiwatar da ayyuka da cinikayya da ma fadada harkoki. Kuma da zarar an samu gogewa da dabaru a nan, to cikin sauki za a shiga kasuwannin ketare.”(Fa’iza Mustapha)














