Majalisar Gudanarwar Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta amince da nadin Dr. Aliyu Dalha Kankia a matsayin sabon Magatakardar jami’ar, yayin da aka nada Yahaya Hussaini a matsayin sabon Bursar.
An amince da naɗin ne a taron musamman na 218 na Majalisar Gudanarwar jami’ar, wanda aka gudanar ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, a ɗakin taron Majalisar da ke Ginin Majalisar Dattawa na ABU, Zariya.
A wata sanarwa da jami’ar ta fitar, an ce Shugaban Majalisar Gudanarwar jami’ar, Mahmud Yayale Ahmed, ne ya sanya hannu kan wasiƙun sanar da jami’an biyu naɗin nasu.
Naɗin zai fara aiki daga ranar 4 ga watan Oktoba, 2026.
Dr. Kankia zai maye gurbin Rabiu Samaila a matsayin Magatakardar jami’ar, yayin da Hussaini zai maye gurbin Mohammed Bello Aminu Gurin a matsayin Bursar.
Dr. Kankia ya yi digirinsa na farko na B.Sc. a Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello, kafin ya samu digirin M.Sc. a International Politics daga Jami’ar Landan da ke Birtaniya.
Ya kuma samu digirin digirgir (PhD) a Kimiyyar Siyasa daga ABU a shekarar 2024.
Ya fara aiki a ABU a ranar 10 ga Disamba, 1990, inda ya samu ɗaukaka a muƙamai daban-daban har ya kai matsayin Mataimakin Magatakarda (Deputy Registrar) kafin nadinsa a matsayin Magatakarda.
Shi kuwa Yahaya Hussaini ƙwararren masani ne a harkokin lissafin kuɗi da gudanar da kuɗaɗe, wanda ke da shekaru 31 na ƙwarewa a fannin kula da kuɗaɗen gwamnati, gudanar da jami’a, kasafin kuɗi, baitulmali da tsarin biyan albashi.
Hussaini ya yi aiki a manyan matakai a Sashen Bursary na jami’ar, inda ya samu ƙwarewa a fannoni daban-daban na harkokin kuɗi da gudanar da jami’a.
Shugabannin jami’ar sun taya sabbin jami’an biyu murna tare da yi musu fatan samun nasara a sabbin mukaman da aka ba su.
Naɗin na zuwa ne a lokacin da ABU ke ci gaba da ƙarfafa tsarin gudanarwa, kula da ma’aikata da kuma tafiyar da harkokin kuɗin jami’ar.












