ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

MURIC Ba Ta Gamsu Da Rahoton Lafiyar El-Rufai Da Aka Gabatar A Kotu Ba

by Sadiq
2 months ago

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana shakku kan rahoton lafiyar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gabatar domin neman beli, tare da yin kira ga kotu da ta gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci.

A cikin wata sanarwa da Shugaban MURIC na Jihar Kano kuma Mai Kula da Jihohin Arewa da Abuja, Malam Hassan Sani Indabawa, ya fitar, ƙungiyar ta ce duk da cewa ta daɗe tana kare haƙƙin El-Rufai, ba za ta yi watsi da gaskiya da adalci ba.

MURIC ta ce buƙatar beli ta uku da lauyoyin El-Rufai suka gabatar ta dogara ne kan rashin lafiya, tare da rahoton lafiya da aka ce Asibitin Ƙasa da ke Abuja ne ya fitar.

ADVERTISEMENT

Sai dai, ƙungiyar ta ce Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Muhammad Raji Mahmud, ya musanta sahihancin rahoton, yana mai cewa ba a fitar da shi da izini ko sanin mahukuntan asibitin ba.

A cewar MURIC, wannan ne ya sa Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar belin a ranar 29 ga watan Yuni, 2026.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ƙungiyar ta ce idan bincike ya tabbatar da cewa an ƙirƙiri rahoton ne, hakan zai kasance abin damuwa matuƙa.

MURIC ta kuma ce tana neman a mutunta haƙƙin El-Rufai, ciki har da ba shi damar ganin iyalansa da kuma samun kulawar likitoci yayin da ake yin shari’ar.

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci kotu ta yanke hukunci bisa hujjoji masu inganci kawai, tare da kira ga lauyoyin El-Rufai su tabbatar da cewa duk takardun da suke gabatarwa sahihai ne.

Haka kuma ta yi kira ga ɓangaren shari’a da ya ci gaba da gudanar da aikinsa ba tare da son rai ko matsin lamba ba.

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
An Kai Kayayyakin Jin Kai Na Gaggawa Na Farko Da Gwamnatin Sin Ta Samar Wa Venezuela

An Kai Kayayyakin Jin Kai Na Gaggawa Na Farko Da Gwamnatin Sin Ta Samar Wa Venezuela

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.