Akalla mutane 24 ne aka ruwaito sun mutu a wasu unguwanni biyu da ke Karamar Hukumar Odigbo a Jihar Ondo, bayan da suka sha wani hadin ganyayyaki da ake zargin yana da illa. Wasu da dama kuma na kwance a asibiti domin karbar magani.
Mutanen da lamarin ya shafa sun fito ne daga Odigbo da Araromi-Obu, yayin da rahotanni suka ce lamarin ya faru a ranar Asabar. Wasu daga cikin wadanda suka sha hadin sun suma kafin daga bisani suka mutu.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Ondo, Dr Banji Ajaka, ya ce gwamnati ta fara bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen. Ya ce har yanzu ba a tabbatar da takamaiman sinadarin da ya jawo mutuwar ba, saboda ana jiran sakamakon gwaje-gwajen lafiya da na na bayanin likita.
Shugaban Karamar Hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya ce an dauki matakan kariya tare da takaita sayarwa da shan wasu hadin ganyayyaki da makamantansu yayin da ake gudanar da bincike. Ya ce jami’an lafiya na gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin mutuwar.
Lamarin ya jawo fargaba da zanga-zangar matasa a yankunan da abin ya shafa, yayin da hukumomi suka bukaci jama’a su guji shan hadin ganyayyaki ko wasu abubuwan sha da ba a tabbatar da ingancinsu ba har sai an kammala binciken.













