Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, ya rasu yana da shekara 91.
Ɗaya daga cikin ’ya’yansa ne ya tabbatar wa maneman labarai rasuwarsa, inda ya ce ya rasu a gidansa da ke Abuja bayan lokaci da ya shafe yana fama da rashin lafiya.
Bamanga Tukur, wanda aka haife shi a Jihar Adamawa a shekarar 1935, ya kasance ɗan siyasa, ɗan kasuwa da kuma ma’aikacin gwamnati da ya riƙe muƙamai daban-daban a Nijeriya.
Ya Taɓa Zama Gwamnan Gongola
Tukur ya zama Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1983.
Jihar Gongola ta haɗa yankunan da daga baya suka zama jihohin Adamawa da Taraba.
Sai dai bai daɗe yana mulki ba, domin sojoji sun karɓi mulki a watan Disamban 1983.
Kafin ya zama gwamna, Tukur ya riƙe babban muƙami a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), inda ya yi aiki a matsayin babban manajan hukumar daga 1975 zuwa 1982.
Ya Taɓa Riƙe Ministan Masana’antu
Tukur ya koma aiki da Gwamnatin Tarayya a shekarun 1990, inda ya taɓa zama Ministan Masana’antu.
Baya ga harkokin siyasa, ya yi fice a fagen kasuwanci kuma ya riƙe muƙamai a ƙungiyoyin kasuwanci na Afirka, ciki har da African Business Roundtable da NEPAD Business Group.
Ya Shugabanci Jam’iyyar PDP
A watan Maris ɗin 2012, an zaɓi Tukur a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, wanda a lokacin ita ce jam’iyyar da ke mulkin Nijeriya.
Ya jagoranci jam’iyyar har zuwa watan Janairun 2014, lokacin da ya yi murabus a yayin da ake fama da rikice-rikice da rarrabuwar kai tsakanin manyan ’ya’yan jam’iyyar.
A lokacin shugabancinsa, wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar PDP da gwamnoni sun samu saɓani da shugabancin jam’iyyar, lamarin da ya kai ga ƙirƙirar wani tsagi a jam’iyyar mai suna “New PDP”.
Rayuwar Bamanga Tukur cike ta ke da tarihi yin aiki a gwamnati, siyasa da kasuwanci, musamman a matakin tarayya da tsohuwar Jihar Gongola.
Shi ne kuma Tafidan Adamawa.














