ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

by Sulaiman
1 hour ago
Gwamnatin Katsina

Gwamna Raɗɗa Ya Gabatar Da Naira Biliyan 829 A Matsayin Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗin ƙarshe a wa’adin mulkin da na farko kimanin Naira Biliyan N828,638,844,091.48 a gaban zauren majalisar dokokin jihar Katsina domin amincewa da shi.

Taken kasafin kuɗin wannan shekara dai shi ne ‘Gina Gobanka Kashi Na 4’ Wanda ya kasance na ƙarshe a wa’adin mulkin da na farko wanda kuma ya bada tabbacin cewa bisa buƙatun al’umma ne ake shirya kasafin kuɗin.

Da yake jawabi a gaban zauren majalisar dokokin jihar Katsina gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa wannan kasafin kuɗin zai maida hankali ne wajen samar da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da ruwan sha da noma da harkar tsaro da sauran abubuwan more rayuwa.

ADVERTISEMENT

“Wannan kasafin kuɗin da muke gabatarwa yanzu, an yi shi ne da hannun al’umma jihar Katsina waɗanda suka bayyana buƙatun su a ya yin taron masu ruwa da tsaki na jin ra’ayoyin jama’a dangane da kasafin kuɗin ” inji shi
A cewar gwamnan an ƙara yawan makarantun sakandare tare da ɗaukar sabbin makaman makarantu waɗanda za su da ce da yanayin koyo da koyarwa a dukkanin makarantu sakandire da ake da su a faɗin jihar Katsina.

Gwamna Raɗɗa wanda ya ce gwamnatin sa ta kashe kimanin Naira Biliyan 3.55 wajen ganewa tare da kula da makarantu na musamman guda uku wanda tuna an fara harkokin karatu cikin ta garin Raɗɗa.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Ya ƙara da cewa an kashe Naira Biliyan 2.07 wajen kuɗin jarabawar ɗalibai ta SSCE da ta haɗa da WAEC da NECO da NABTEB da kuma NBAIS tare da haɗin gwiwa da ƙananan hukumomi 34 sannan ya ƙara da cewa kimanin Naira Miliyan 1.26 an kashe su wajen bada tallafin karatu ga ɗalibai na cikin gida da kuma na ƙasashen waje.

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya ƙara da cewa a wannan shekarar ta 2026 gwamnatin sa ta bada tallata mata daban-daban a ƙananan hukumomi 34 tare da bada tallafin sana’o’i ga matasa domin su dogara da kan su.

Dangane da batun tsaro kuwa gwamnan ya bayyana cewa an samu sauki so sai inda ya ce manoma sun koma gonakin su a wannan shekara domin yin noma wanda hakan ke nuna irin nasarorin da aka samu.

A ɓangaren kiwon lafiya ya ce babu wata mazaɓa cikin 361 da ake da su a faɗin jihar Katsina da babu wata cibiyar kiwon lafiya wanda yake aiki kowane lokaci.

Akan batun kiwon lafiya kuwa, gwamnan ya ce tsakanin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da manyan asibitoci guda 1,751 sun kai kashi 85 na ɗaukaka darajar su

Kazalika ya ƙara da cewa an kashe kuɗi Naira Biliyan 4.71 wajen samar da ayyukan kiwon na gaggawa tare da sayi motocin ɗaukar marasa lafiya tare da zuba jari a wasu asibitoci da magunguna da gine-gine.

Malam Dikko Raɗɗa ya ce ɓangaren ruwan sha kuwa gwamnatin sa tana cikin wani ƙoƙari wanda yake aiki jawo ruwan Zobe Dam da zai ratsa ƙananan hukumomi 8 da za su amfana da ruwan sha mai tsafta dukkanin su.

Haka kuma gwamna Raɗɗa ya nuna buƙatar da ake da ita, wajen cigaba da samar da tsabtataccen ruwan sha inda ya bayyana cewa rijiyoyin burtsatse na nan a matsayin hanyar samar da ruwan sha ga mafiyawan magidanta
Ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata cigaba da tabbatar da wata zuba jari a ɓangaren ruwan sha tare da ƙoƙarin kai ruwa wurare daban-daban a ƙarƙashin shirin samar da ruwan sha na Zobe Phase 1B Water Project.

Tunda farko da yake jawabi kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Nasiru Yahaya Daura ya yaba da ɓangaren zartawar dangane da yin amfani da kasafin kuɗin shekarar da ake ciki ta 2026.

Haka kuma ya bada tabbacin cewa majalisar zata cigaba da bada goyon baya ga ɓangaren zartawar domin a samu nasarar da ake buƙata wajen aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2027.
Hon. Nasiru Yahaya Daura wanda ya yi bayanin cewa kwamitin tantance kasafin kuɗin majalisar zai yi aikin ba tare da ɓata lokaci ba ta yadda za a kammala kare kasafin kuɗin cikin lokaci kamar yadda aka saba.

Radda
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara
  • Sulaiman
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

MASU ALAKA

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan
Labarai

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati
Labarai

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Next Post
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

LABARAI MASU NASABA

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.