Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon ƙarin albashin jami’an soji a cikin makonni masu zuwa, kamar yadda Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana.
Ministan ya ce ƙarin albashin da ake shirin yi na daga cikin manyan ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta jin daɗin jami’an Rundunar Sojin Nijeriya da kuma amincewa da irin haɗarin da suke fuskanta wajen kare ƙasa.
Da yake magana ranar Litinin a Abuja yayin wani shirin horarwa da ƙarfafa wa mata da mazansu ke aikin soja suka rasu, Musa ya ce tuni gwamnatin ta ƙara albashin sojoji daga kusan Naira 49,000 zuwa Naira 100,000, kuma yanzu tana shirin sake duba albashin.
Shekaru da dama, jami’an soji da ke aiki da waɗanda suka yi ritaya sun yi ta suka kan tsohon mafi ƙarancin albashin wata-wata na kusan Naira 49,000, suna cewa bai isa biyan buƙatun yau da kullum ba, musamman sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, ƙarin kuɗin sufuri da tashin farashin kayan abinci.
Masana harkokin ƙwadago da tsaro su ma sun yi iƙirarin cewa albashin bai yi daidai da irin haɗarin da sojojin da aka tura ayyukan yaƙi da ta’addanci, ƴan bindiga da sauran ayyukan tsaron cikin gida ke fuskanta ba.
Duk da cewa ƙarin albashin zuwa Naira 100,000 ya kasance gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da tsohon albashin, masana tattalin arziki sun bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya na ci gaba da rage ƙarfin darajar wannan kuɗi.
Tun bayan ƙarin albashin, farashin muhimman kayan abinci, sufuri, gidaje da sauran hidimomin yau da kullum ya ci gaba da kasancewa a sama, wanda ke nufin cewa Naira 100,000 a halin yanzu ba ta da irin ƙarfin saye da take da shi a ƴan shekarun da suka gabata.
Hakan ya sake haifar da kiraye-kirayen a riƙa duba albashin jami’an soji lokaci-lokaci domin ya dace da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.














