ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙyamar Baƙi: Tinubu Ya Ƙi Ganawa Da Jakadan Afirka Ta Kudu

by Sulaiman
1 month ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙi karɓar wata tawaga ta musamman da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aiko kan hare-haren ƙyamar baƙi da aka sake kai wa ƴan Nijeriya da sauran ƴan Afirka a Afirka ta Kudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa a maimakon haka, Shugaban Ƙasan ya umarci wakilan da suka zo da su gana da Ministan Ƙasa na Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye.

Majiyoyin da suka san da lamarin sun ce tawagar, wadda Ministan Harkokin Ƙasa da Haɗin Kan Ƙasa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ke jagoranta, ta isa Abuja a ƙarshen mako ɗauke da saƙo daga Shugaba Ramaphosa.

ADVERTISEMENT

Sai dai an umarci tawagar da ta je Ma’aikatar Harkokin Waje domin miƙa saƙon ga ministan.

Da aka tuntuɓe shi, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya tabbatar wa Daily Trust da faruwar lamarin.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Onanuga ya ce wakilin ya iso ranar Juma’a ba tare da sanar da gwamnatin Nijeriya tun da wuri ba, kuma ya dage sai ya gana da Shugaba Tinubu domin miƙa masa saƙon da kansa.

Ya ce jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje sun ɗauki wannan buƙata a matsayin wadda ba ta dace ba.“Da farko dai, wakilin ya iso ranar Juma’a ba tare da sanar da gwamnatin Nijeriya tun da wuri ba. Ya dage cewa sai ya gana da Shugaban Ƙasa ranar Juma’a domin miƙa masa saƙonsa.

“Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce wannan buƙata ba ta dace ba. Ma’aikatar ta tsara ganawar ranar Litinin. Amma Shugaba Tinubu ya nemi wakilin da ya miƙa saƙonsa ga Ministan Harkokin Waje,” in ji Onanuga.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya umarci Ministan Ƙasa na Harkokin Waje, Ambasada Enikanolaiye, da ya tattauna da wakilin tare da yi masa bayani daga bisani.

A kwanakin nan, ƴan Nijeriya da sauran ƴan ƙasashen Afirka sun sake fuskantar hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

MASU ALAKA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
Labarai

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Next Post
Tinubu

Gwamnatin Kano Ta Nemi A Saki Tallafin ₦5bn Na Gobarar Ƴan Kasuwar Singa

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.