Hukumar NDLEA reshen jihar Kano ta gargadi iyaye kan yaɗuwar alewa da cincin da ake zargin suna ɗauke da sinadaran maye.
Wannan gargadi ya fito ne ta cikin wani bidiyo da kakakin hukumar, ASN Sadiq Maigatari, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- NDLEA Ta Kama Mutane 415, Ta Ƙwace Tan 1.2 Na Ƙwayoyi A Bauchi
- NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa
A cikin bidiyon, Maigatari ya bayyana cewa wasu alewoyi da suka yi kama da cakuleti na yau da kullum suna ɗauke da sinadarai masu sa maye, kuma ana sayar da su ga yara ba tare da sun sani ba.
Ya Buƙaci iyaye su riƙa duba sinadaran da aka haɗa da kayan zaƙi da cocin da ‘ya’yansu ke ci ko sha, domin kaucewa haɗarin shan kwayoyi.
“Ina so iyaye su lura da alamomin ganye ko wasu alamomi masu alaƙa da tabar wiwi da ake iya gani a jikin kwali ko murfin kayan zaƙin. Ya zama dole su kasance masu taka tsantsan domin kare ‘ya’yansu daga shan irin waɗannan abubuwa,”
in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp