Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya ce ba shi da wata shaida da za ta tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023, amma har yanzu yana da yaƙinin cewa shi ne ya yi nasara.
Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Africa, inda ya yi magana kan dalilin da ya sa yake shirin sake tsayawa takara a zaɓen 2027.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana da hujjar da za ta tabbatar da cewa ya lashe zaɓen, tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce, “Babu shaida… amma na lashe zaɓen.”
Obi ya kuma ci gaba da cewa an tafka maguɗi a zaɓen 2023, duk da cewa kotuna sun yi watsi da ƙarar da ya shigar.
A zaɓen 2023, Obi ya tsaya takara ne ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party, inda ya zo na uku da ƙuri’u 6,101,533.
Hukumar INEC ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 8,794,726, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu da ƙuri’u 6,984,520.
Obi da Labour Party sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen, suna zargin an samu kura-kurai da kuma take dokokin zaɓe.
Sai dai Kotun Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ƙarar a watan Satumban 2023, sannan Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin a watan Oktoban shekarar.
Duk da hukuncin kotunan, Obi ya ci gaba da cewa sakamakon zaɓen bai nuna ainihin ra’ayin masu zaɓe a Nijeriya ba.
Yanzu haka yana shirin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, a wannan karon a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.














