ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ni Ne Wanda Sir Aleɗ Ya Fara Zaɓa Zan Maye Gurbinsa A 2013 – Mourinho

by Abba Ibrahim Wada
4 weeks ago
Mourinho

Bayan shekaru da dama ana jita-jita, Jose Mourinho ya tabbatar da cewa ya amince ya maye gurbin mai koyarwa Sir Aleɗ Ferguson a Manchester United, kafin daga bisani ya sauya ra’ayi ya koma Chelsea. Lokacin da Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013 bayan shekaru 26 a Old Trafford, ya ba da shawarar a naɗa Daɓid Moyes, wanda a lokacin shi ne kocin Eɓerton, a matsayin magajinsa.

Wannan ne ya sa aka yi wa Moyes laƙabi da “The Chosen One” wanda aka Zaɓa, har ma an rataye wani babban allo mai ɗauke da wannan suna a ɓangaren Stretford End na filin wasan ƙungiyar.

Da yake magana a cikin wani sabon shirin tarihin rayuwarsa da za a fara nunawa a Netfliɗ daga 11 ga Agusta, Mourinho ya ce lokacin da ya bar Real Madrid, ya amince da zuwa Manchester United domin maye gurbin Sir Aleɗ.

ADVERTISEMENT

Ferguson, wanda ya lashe Premier League 13 a matsayin kocin United, ya tabbatar da cewa an miƙa wa Mourinho aikin. Ya ce: “Na zaunar da shi na yi masa bayanin halin da ake ciki. A ganina, ya amince da karɓi aikin. Amma cikin sa’o’i kaɗan komai ya sauya.”

Abin da ya sauya kuwa shi ne Mourinho ya ji cewa ba zai koma Chelsea ba da aiki, inda a nan ne ya taɓa lashe kofunan Premier League a jere a shekarun 2005 da 2006.

LABARAI MASU NASABA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ferguson ya ƙara da cewa: “A wani dare ya kira ni yana kuka, sai ya ce, ‘Aleɗ, ba zan iya karɓar aikin nan ba. Na riga na yi wa Chelsea alƙawari kuma ba zan karya alƙawarina ba.’“Dalilin da ya ba ni na fahimta, amma duk da haka na ji ba dadi.”

Mourinho, mai shekaru 63, ya ce ya ji matuƙar karramawa da aka ba shi damar maye gurbin Ferguson saboda: “Manchester United ƙungiya ce mai matuƙar jan hankali.”

“Rashin damar zama kocin da zai gaji Sir Aleɗ Ferguson abu ne mai raɗaɗi a gare ni, amma ban taɓa nadama ba domin shawara ce da na yanke a zuciyata.”

Bayan komawarsa Stamford Bridge a shekarar 2013, Mourinho ya lashe kofina uku na Premier League tare da Kofin League Cup. A gefe guda kuma, an sallami Daɓid Moyes daga aikin bayan watanni goma kacal a matsayin kocin Manchester United. Daga baya, Mourinho ya samu wata dama ta biyu ta jagorantar United a shekarar 2016, inda ya maye gurbin Louis ɓan Gaal.

A tsawon shekaru biyu da rabi da ya yi a Old Trafford, Mourinho ya lashe League Cup da Europa League kafin a kore shi a watan Disamban 2018 biyo koma bayan sakamako da ƙungiyar ta samu.

Mourinho
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
Wasanni

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Next Post
Tsakanin Shinkafa Da Miya Da Dafaduka (Jolof Rice) Wanne Ka Fi So?

Tsakanin Shinkafa Da Miya Da Dafaduka (Jolof Rice) Wanne Ka Fi So?

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.