A wannan karon ma, mun sake tattaro ra’ayoyin masu karatu, don sanin kalar abincin da ya fi birge su, tsakanin shinkafa da miya da kuma dafaduka (Jolof Rice). SANI ANWAR da MUHAMMAD BAƘIR ne, suka tattara waɗannan ra’ayoyi.
Mahadi Isa Waziri daga Zaria
Na fi son shinkafa da miya, saboda ya fi min daɗi, kuma ina ganin ya fi lafiya a jiki fiye da mai mai da yaji, musamman ga masu ciwon ulsa.
Sannan kuma, yawan cin mai ba shi da amfani ga lafiyar Ɗan’adam, shi ya sa nake ganin cewa; mai miya ya fi mai mai amfani, musamman ga lafiya.
Koda-yake, na kan ci mai mai ɗin, lokaci bayan lokaci idan na yi marmari, amma dai batu na gaskiya na fi son mai miya fiye da mai mai ɗin.
Hamid Awwal, daga Zaria
A halin da nake ciki yanzu, ma’ana a matsayina na ɗan makaranta, shinkafa da mai da yaji ta zama wata hanya ta samun sauƙi, domin kuwa tana taimaka min wajen rage kashe kuɗi da kuma lokaci. Koda ba ka son abu, in dai za ka yi ta maimaita shi sau ba adadi, ba za ka san san da wannan kiyayyar za ta zama soyayya mai ƙarfi a gare ka ba. A yanzu, na fi son in dafa farar shinkafa da wake, na yanka mata kayan miya ta ji mai da yaji sosai, idan da hali na yanka dafaffen ƙwai a kai, wadda ta fi min shinkafa damiya daɗi ƙwarai da gaske.
Ina iya shafe faranti biyu, sannan na danna da ruwan sanyi. Duk da na san illa ne ga lafiyata, amma babu cutar da ba ta da magani. Shi ya sa ba na rabuwa da magani a kusa da ni a koda-yaushe.
Aisha Usman, daga Maiduguri
Ni dai na fi son shinkafa da miya, musamman idan miyar da naman kaza ko naman akuya shaƙe a ciki. Koda-yake, ita ma dafadukan (Jolof Rice), ba a bar ta a baya ba, amma duk inda na samu shinkafa da miya na fuskance ta yadda kamata, ranar ba a cewa komai, sai hamdala. Na gode.
Abdullahi Sale, daga Abuja
Ko shakka babu, na fi son shinkafa da miya, musamman idan aka haɗa ta da salak da tumatir da albasa, sannan kuma ta sha dabgen naman kai a kai. Da zarar hakan ta samu, to fa yau take Sallah, domin kuwa ba za a bai wa yaro mai ƙiwa ba.
Gaskiya a matsayina na magidanci, ina matuƙar jin daɗin shinkafa da miya kamar yadda na bayyana a baya. Shi ya sa idan uwargida na son birge ni, shi ne abin da takan shirya min a matsayin bazata.
Hamza Abdullahi, daga Jihar Kano
Na fi son shinkafa da miya, musamman miyar da za a yi da ɗanyen tattasai da tumatir, ba busasshe ba. Haka zalika, ina so na ga an yanka tattasai da tumatir a kai ga kuma tantaƙwashin nama da ƙyafaffen naman kaza a kai.
Wato bayan an soya kaza ta soyu, sannan kuma sai a zuba ta a cikin miya ta dahu lugub. Da zarar hakan ta samu, komai lafiya-lafiya kenan.
Hamidat Yahaya, daga Jihar Kwara
Gaskiya na fi son dafadukan shinkafa (Jolof Rice), dalili kuwa shi ne, ta fi min sauƙin sarrafawa. A duk lokacin da nake son dafa shinkafa da miya, dole ne sai na nemi kifi ko nama da sauran dangoginsu, idan har ina so abincina ya yi daɗi. Amma shinkafa dafaduka, ba ta buƙatar wasu tsarabe-tsare masu yawa.
Da zarar ka ɗan samu kayan miyarka da magi da gishiri, wasu ma su kan saka daddawa a ciki, nan take za ka dafa abincinka mai rai da lafiya, ba tare da wani ɓata lokaci ko kashe kuɗaɗe masu yawa ba.














