• Leadership Hausa
Friday, August 19, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

NIS Ta Sauya Wuraren Aiki Ga Manyan Jami’ai 69

by Abdulrazaq Yahuza
2 weeks ago
in Labarai
0
NIS Ta Sauya Wuraren Aiki Ga Manyan Jami’ai 69
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), CGI Isah Jere Idris, ya amince da sauya wuraren aiki ga manyan jami’ai 69 zuwa manyan ofisoshin hukumar na shiyyoyi da jihohi da ke sassan ƙasar nan.

  • NIS Reshen Jihar Bayelsa Za Ta Fara Bayar Da Sabon Ingantaccen Fasfo

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACI Amos Okpu ta bayyana cewa daga cikin adadin jami’an da aka sauya wa wuraren aikin akwai masu muƙaman ƙananan Mataimakan Kwanturola Janar (ACG) guda takwas sai masu muƙaman Kwanturololi (CIS) guda 61 da aka rarraba su a sassan manyan ofisoshin hukumar.

Cikin masu muƙaman ACG da aka sauya wa wuraren aikin akwai ACG KM Amao wanda a da yake Kwanturolan Jihar Ogun amma yanzu an maida shi Sashen Ayyuka Na Gaba ɗaya a shalkwatar hukumar da ke Abuja, sa’ilin da ACG KN Nandap wanda a baya yake kula da Babban Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas a yanzu kuma aka sauya masa zuwa Sashen Bayar da Takardu ga Baƙin Waje (CERPAC) a shalkwata.

Har ila yau, ACG Abdullahi M Usman a yanzu shi ne Shugaban Sashen Kula da Shige da Fice na Yau da Kullum a shalkwatar hukumar, yayin da ACG BN Alawode ya zama Shugaban Sashen Kula da Walwala da Daidaiton Jinsi, sai kuma ACG EC Esedo da aka mayar zuwa Ofishin Shiyya ta huɗu da ke Minna.
Shi kuwa ACG MA Ushie na Sashen Yaƙi da Damfara an mayar da shi zuwa Sashen Difilomasiyya da Fasfo, sai ACG ES Fagbamigbe wanda a da yake kula da Babban ofishin Iyaka na Idi-Iroko da aka tura ya zama shugaban kula da iyakokin ƙasa na kan-tudu a shalkwata.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

Darussa Daga Gwagwarmayar Kasar Sri Lanka (Nazari)

Daga cikin masu muƙaman Kwanturololi da aka sauya wa wuraren aikin kuwa akwai Compt. AO Adesokan da aka mayar zuwa Babban Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Legas daga Sashen Horaswa da Inganta ƙwazon Ma’aikata, yayin da muƙaddashin babban jami’in ofoshin Kwanturola Janar, Compt. Ahmed Mustapha ya zama sabon Kwanturolan Kano. Sauran sun haɗa da Compt. Shittu Olajire Fatai wanda a yanzu aka mayar da shi Ofishin Kula da Iyaka na Legas; da Compt. Gwama Muhammad wanda a yanzu shi aka ba shugabancin Ofishin kula da iyaka na Idi-Iroko; da Compt. MM Saddiƙ wanda a yanzu aka ba shi matsayin Babban Jami’in Ofishin Kwanturola Janar.

Shi kuwa Compt. AO Bewaji an mayar da shi ne zuwa shalkwatar hukumar yayin da Compt. Michael Dike ya karɓi ragama a matsayin Kwanturolan Iyaka na Seme da ke Legas. Shi kuwa Kwanturola mai kula da ɗa’ar aiki an tura shi ya shugabanci yankin Jihar Osun yayin da Compt. Sabo A Rano da ya kasance Kwamandan Makarantar Horas da Jami’ai ta Kano aka mayar da shi zuwa Jihar Gombe.

Bugu da ƙari, Compt. FD Dakat na Sashen kula da tasoshin ruwa aka mayar da shi zuwa Jihar Akwa Ibom inda zai karɓi ragama daga Compt. GE Didel wanda aka mayar zuwa sashen shige da fice a shalkwata, da dai sauransu.

Shugaban Hukumar ta NIS, Isah Jere ya hori dukkan jami’an da aka sauya wa wuraren aikin su yi amfani da basirar da Allah ya yi musu a wuraren da aka tura su wajen inganta aiki da tsaron ƙasa. Sauyin aikin dai ya fara aiki ne nan take.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Bisa Aiki Tukuru Sin Ta Samu Karbuwa A Kasashen Afirka

Next Post

Jami’an Diflomasiyyar Afirka Na Fatan Kara Kulla Huldar Tattalin Arziki Da Kasar Sin

Related

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa
Kananan Labarai

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

29 mins ago
srilanka
Rahotonni

Darussa Daga Gwagwarmayar Kasar Sri Lanka (Nazari)

2 hours ago
Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki
Labarai

Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki

3 hours ago
Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu
Labarai

Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu

4 hours ago
Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…
Rahotonni

Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…

5 hours ago
Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim
Labarai

Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim

6 hours ago
Next Post
Jami’an Diflomasiyyar Afirka Na Fatan Kara Kulla Huldar Tattalin Arziki Da Kasar Sin

Jami’an Diflomasiyyar Afirka Na Fatan Kara Kulla Huldar Tattalin Arziki Da Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

Yadda Aka Sace Kwamishina A Nasarawa

August 19, 2022
Nadin Kwamishinoni A Kano: Kar A Yi Kitso Da Kwarkwata

Nadin Kwamishinoni A Kano: Kar A Yi Kitso Da Kwarkwata

August 19, 2022
Da Dumi-Duminsa: NBC Ta Soke Lasisin Tashoshin AIT, Silverbird TV Da Wasu 50

Da Dumi-Duminsa: NBC Ta Soke Lasisin Tashoshin AIT, Silverbird TV Da Wasu 50

August 19, 2022
srilanka

Darussa Daga Gwagwarmayar Kasar Sri Lanka (Nazari)

August 19, 2022
Goro

Goron Jumu’a

August 19, 2022
Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki

Nunez Ya Jika Wa Liverpool Aiki

August 19, 2022
Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu

Kamata Ya Yi Dalibai Su Maka Kungiyar ASUU A Kotu Kan Bata Musu Lokaci—Adamu Adamu

August 19, 2022
Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…

Kusan Shekara 100 Da Kafa Asibitin Kutare Na Kano, Amma…

August 19, 2022
Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim

Son Zuciyar Wasu Tsiraru Ya Haddasa Rashin Tsaro A NIjeriya – Alhaji Ibrahim

August 19, 2022
Kokarin CBN Wajen Daga Darajar Naira

Kokarin CBN Wajen Daga Darajar Naira

August 19, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.