ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Damar Fita Daga Kangin Dalar Amurka Ta Sake Samuwa Ga Kasashen Afirka

by Sulaiman
2 months ago
Amurka

A cikin tattalin arzikin duniya na yau, samun saukin gudanar da harkokin kudi ya zama muhimmin ginshiki wajen bunkasa kasuwanci tsakanin kasashe. Ba wai yawan kayayyakin da kasashe ke sayarwa da siya kawai ke kayyade karfin alakar tattalin arziki ba, tsarin biyan kudi, farashin hada-hadar kasuwanci, da saukin samun canjin kudi suna taka muhimmiyar rawa.

A wannan mahangar ce ake kallon amincewar da Babban Bankin Jama’ar Sin ya yi kwanan nan ga Bankin Standard na Afirka ta Kudu da kuma Bankin ICBC na kasar Sin, su gudanar da aiki cikin hadin gwiwa a matsayin bankin saukaka samun kudin RMB, ya zama wani muhimmin mataki da zai zurfafa hadin gwiwar tattalin arzikin Sin da Afirka.Tsarin zai ba kamfanoni da cibiyoyin kudi daga kasashen Afirka 19 damar gudanar da hada-hadar kudin yuan (RMB) kai-tsaye a bisa tsarin kudin cikin gida na Sin, abin da zai iya rage wasu matsalolin da ke tattare da biyan kudin ciniki da zuba jari ta amfani da dalar Amurka. Wannan shi ne karo na farko da aka bai wa wata cibiyar kudi a Afirka irin wannan cikakkiyar dama ta saukaka samun kudin RMB a nahiyar.

Tsawon shekaru dai, dalar Amurka ta kasance babbar hanyar gudanar da cinikayyar duniya, amma ga kasashe masu tasowa kamar na Afirka, dogaro da dala ya kara jefa su tsaka-mai-wuya saboda yanayin tattalin arzikinsu na shigo da kayayyaki. Don haka, a kasuwancin Sin da Afirka, amfani da dala ya kara tsawaita tsarin hada-hadar kudi. Mai sayarwa a Afirka da mai saye a Sin na iya fuskantar bukatar canza kudi daga wani nau’in kudi zuwa wani kafin a kammala ciniki, inda hakan yake haifar da jinkirin kammala biyan kudi da kuma fargabar hawa da saukar dalar.

ADVERTISEMENT

Wasu rahotannin nazarin kasuwanci, sun nuna cewa amfani da RMB kai-tsaye zai iya taimakawa wajen kauce wa wasu daga cikin wadannan karin matakai, domin kamfanonin Afirka za su iya biyan kudin kayayyaki daga Sin da yuan kai-tsaye maimakon dogaro da tsarin dala. Wannan mataki dai ya zo ne a lokacin da dangantakar tattalin arzikin Sin da Afirka ke kara karfi musamman ma bayan shirin soke biyan harajin kwastam na kasar Sin ga kayayyakin kasashen Afirka 53 masu alakar diflomasiyya da ita, da ake shigarwa kasuwanninta. Hade tsarin saukaka kasuwanci da na biyan kudi na iya samar da wani sabon yanayi da zai taimaka wajen fadada ciniki tsakanin bangarorin biyu.

Masu fitar da kayayyaki daga Afirka, musamman a fannoni kamar noma, ma’adanai, da kayayyakin masana’antu, na iya amfana daga wannan tsarin da zai rage matsalolin kudi da kuma fita daga kangin dala, saboda samun karin zabi na biyan kudin hada-hada zai kara masu saukin gudanar da kasuwanci har ma da taimaka wa gwamnatocinsu wajen tsara manufofin kasuwancinsu.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Nasarar wannan shiri dai ba za ta tsaya ga saukaka biyan kudi ba, har ma da taimaka wa Afirka bunkasa masana’antu, da fitar da kayayyakin da aka sarrafa, da inganta gina kasuwanci mai daidaito wadanda suka samu tazgaro saboda kangin dala da tsarin kasuwancin duniya mai siffar kashin Dankali. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Amurka
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.