Ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), reshen Babban Birnin Tarayya, ta tsunduma yajin aikin sai baba-ya-gani a faɗin Abuja daga ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan gazawar Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) wajen warware matsalolin da suka daɗe suna addabar malamai, ciki har da jinkirin ƙarin matsayi, tsaiko wajen ci gaban aiki da kuma sauya wajen aikin wasu daraktocin makarantu.
NLC na buƙatar FCTA ta cire sharadin samun guraben aiki kafin a ɗaukaka matsayin malamai, tare da bai wa malaman da suka cancanci ɗaukaka matsayinsu a 2025 damar rubuta jarabawar tare da waɗanda suka cancanta a 2026.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci a janye wasiƙun sauya wajen aiki da rage matsayi da aka bai wa wasu daraktocin makarantu, tare da rushe kwamitocin gudanarwa na makarantun babban birnin tarayya.
NLC ta bayyana martanin FCTA kan buƙatunta a matsayin wanda bai gamsar ba.
Sannan ta umarci ma’aikata a ofisoshin gwamnati, makarantu, asibitoci da sauran hukumomi da su dakatar da ayyukansu har sai an warware matsalolin.














