A ranar Litinin aka karkare kakar kallon fina-finai ta bazara ta shekarar 2026 a kasar Sin, inda aka tara kudin shiga da ya kai kusan Yuan biliyan 12 da rabi, kwatankwacin dala biliyan daya da miliyan 84, wanda ya dan karu daga kusan biliyan 12 da ake samu shekara-shekara.
Hukumar da ke kula da harkokin tafiyar da fina-finai ta kasar Sin ce ta bayyana haka, inda ta ce wannan ci gaba ya nuna yadda kallon fina-finai ke bunkasa cikin shekaru biyu a jere, wanda ake gudanarwa a tsakanin watan Yuni zuwa Agusta.
Adadin makallata ya kai kusan kudin Sin yuan miliyan 340 kari kan yadda aka samu a shekarar 2025, inda aka samu makallata miliyan 321, kazalika a shekararar 2024 aka samu yawan makallata miliyan 284. (Suleiman Suleiman Ibrahim)














