Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wasu mutane shida ’yan asalin Kudu maso Gabashin Nijeriya bisa zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi da aka kiyasta darajarsu ta kai Naira miliyan 500 a Jihar Kano.
A wani rahoto da jaridar Kano Times ta buga, ta bayyana sunayen wadanda aka kama da Onyeka Vincent, Success Chibuzie, Nwankwo Wisdom, Emmanuel Jude, Chinedu Peter da Okodili Ogbuach, bayan jami’an NDLEA sun tare wata motar bas ta fasinjoji a wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a watan Agusta.
A yayin samamen, jami’an hukumar sun kuma kwace motar bas din, wadda ake zargin tana da alaka da safarar miyagun kwayoyin.
Sai dai an samu rahotannin cewa motar, wadda ake cewa mallakin wani fitaccen dan kasuwa ne daga Kudu maso Gabas, na cikin motocin da ake duba yiwuwar sakin su duk da cewa ana cigaba da bincike kan zargin.
Sai dai Shugaban Rundunar Musamman ta Jihar Kano kan Yaki da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi, Muhuyi Magaji, ya yi watsi da wadannan rahotanni, yana mai cewa, har yanzu ana kan gudanar da bincike kan lamarin.














