Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin, Xi Jinping, da Aigul Japarova, uwargidan shugaban kasar Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, sun ziyarci gidan tarihi na kasa na jamhuriyar Kyrgyzstan a yau Litinin.
Peng da Japarova sun kalli wasan maraba da baki tare, kafin daga bisani sun ziyarci wurin baje kolin al’adun gargajiya na kasar Kyrgyzstan.
Peng ta bayyana cewa, kayan ado, da darduma da sauran abubuwan da aka baje kolinsu, wadanda aka saka su cikin kaifin basira da kyau tare da launuka masu kayatarwa, sun nuna dadaddun sana’o’in hannu na kayan gargajiya da kuma dabi’u na musamman na al’ummar Kyrgyzstan.
Ta ce duka kasashen Sin da Kyrgyzstan suna ba da muhimmanci sosai wajen kiyayewa da kuma gadar da al’adun gargajiya, inda ta bayyana fatan cewa kasashen biyu za su ci gaba da fadada mu’amala tsakanin al’ummominsu da musayar al’adu, tare da kara karfafa zumunci a tsakanin jama’arsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














