Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa da jin labarin ceto mambobin NYSC 15 da wasu ’yan Nijeriya shida da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kogi.
Tinubu, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, ya ce an samu nasarar ceto mutanen 21 da aka yi garkuwa da su ne a yammacin ranar Litinin, bayan wani aikin hadin gwiwa na bincike da ceto da hukumomin tsaro da ’yan banga na yankin suka gudanar.
Ya ce wadanda aka ceto, wadanda suka hada da maza takwas da mata 13, an same su ne a maboyar masu garkuwa da mutane da ke cikin dazuzzukan Karamar Hukumar Ofu ta jihar.
Shugaban kasar ya ce, “Na yi matukar farin ciki da samun labarin cewa mambobin NYSC 15 da wasu ’yan Nijeriya shida, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kogi a makon da ya gabata, sun samu ‘yancinsu.”














