Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya rubuta wasiƙa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya roƙe shi da ya taimaka wa ’yan kasuwar Filin Idi da ke Kofar Mata, waɗanda aka ruguza wa shaguna.
Shugaban Ƙungiyar Masu Shagunan Filin Idi, Auwal Sa’id Umar, ne ya bayyana hakan yayin taron addu’ar da ’yan kasuwar suka gudanar a wurin.
A cewarsa, Sarkin ya roƙi gwamnan da ya biya ’yan kasuwar diyya tare da samar musu da wuraren da za su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Auwal ya gode wa Sarkin bisa shiga tsakani da ya yi, sannan ya yaba wa Gwamna Abba kan ware shaguna 75 domin sake gina kasuwancin waɗanda abin ya shafa.
Sai dai ya bayyana cewa shagunan 75 ɗin sun kai kashi 25 cikin 100 ne kawai na jimillar shagunan da ake buƙata a filin, yana mai cewa da dama daga cikin ’yan kasuwar ba su da isassun kuɗaɗen da za su gina sababbin shaguna.
Ya roƙi gwamnatin jihar da ta ƙara tallafa musu, yana mai cewa rugujewar shagunan ta shafi sana’o’insu da hanyoyin da suke samun abin biyan buƙatun iyalansu.
Auwal ya ce samar da ƙarin tallafi zai taimaka wa ’yan kasuwar wajen farfaɗo da harkokinsu na kasuwanci da kuma rage matsalolin tattalin arzikin da suke fuskanta sakamakon rusau ɗin.
Taron ya kuma kasance wani ɓangare na bikin saukar Alƙur’ani mai girma karo na 111, inda aka gudanar da addu’o’in samun nasara ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da Gwamna Abba Kabir Yusuf.














