ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kashe Masu Garkuwa 2, Sun Ceto Wanda Aka Sace, Da Kwato Naira Miliyan 10 A Kano

by Muhammad
3 weeks ago

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane, sun ceto wani mutum da aka sace, sannan sun kwato Naira miliyan 10 da aka biya a matsayin kuɗin fansa a dajin Falgore da ke Ƙaramar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano.

Dakarun Birged ta Uku ne suka gudanar da aikin a ƙarƙashin Operation MESA, bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Fanyabo da ke cikin dajin Falgore a ranar 11 ga Oktoba, 2026.

A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji na Birged ta Uku, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar a ranar Asabar, ya ce an sace Aliyu ne lokacin da yake dawowa daga Kasuwar Yandoka da ke Jihar Kaduna da tsakar dare.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta bayyana cewa bayan sace shi, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa da ke ƙauyen Yan Taburmi, shi ma a cikin dajin Falgore, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa domin sakin sa.

Bisa ga sanarwar, dakarun sojojin sun samu sahihan bayanan sirri game da lamarin, sannan suka shirya kwanton-ɓauna tare da haɗin gwiwar ’yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da mafarautan yankin.

LABARAI MASU NASABA

An Jikkata Mutane, An Lalata Motocin Kamfen A Taron Obi Da Kwankwaso A Delta

Sabon Hukuncin Kotu Kan ADC Na Iya Janyo Yaƙin Basasa — Amaechi

Sanarwar ta ce aikin ya yi nasarar kashe mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto wanda aka sace, yayin da sauran mambobin ƙungiyar suka tsere zuwa cikin dajin Falgore.

Ta ƙara da cewa bayan haka, dakarun sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano Naira miliyan 10 da ake zargin iyalan wanda aka sace sun biya a matsayin kuɗin fansa.

Sanarwar ta ce an mayar da kuɗin ga wanda aka ceto da iyalansa.

Kwamandan Birged ta Uku, Birgediya-Janar Saka Jimoh, ya yaba wa dakarun bisa jajircewarsu, ƙwarewa da kuma ƙwazon da suka nuna yayin gudanar da aikin.

Jimoh ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka da kuma hana sake samun barazanar tsaro a yankin.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro a kan lokaci, domin taimakawa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Ƙarancin Ruwa Da Iskar Gas Ne Sanadin Raguwar Samun Wutar Lantarki A Nijeriya
  • Muhammad
    Wane Tasiri Ƙarin Ciyo Bashin Dala Biliyan 7.7 Zai Yi A Kasafin Kuɗin Nijeriya Na Gaba?
  • Muhammad
    Rikicin Siyasa: Shin ’Yan Takarar Jam’iyyun Adawa Suna Samun Tsaron Da Ya Dace A Yaƙin Neman Zaɓen 2027?
  • Muhammad
    Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

MASU ALAKA

An Jikkata Mutane, An Lalata Motocin Kamfen A Taron Obi Da Kwankwaso A Delta
Manyan Labarai

An Jikkata Mutane, An Lalata Motocin Kamfen A Taron Obi Da Kwankwaso A Delta

November 8, 2026
Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
Labarai

Sabon Hukuncin Kotu Kan ADC Na Iya Janyo Yaƙin Basasa — Amaechi

November 8, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira
Manyan Labarai

Zaɓen 2027 Zai Fayyace Makomar Matasa — Tinubu

November 8, 2026
Next Post
2027: Gwamna Radda Ya Nemi Afuwar Waɗanda Ya Ɓata Wa Rai, Ya Buƙaci Haɗin Kan APC A Katsina

2027: Gwamna Radda Ya Nemi Afuwar Waɗanda Ya Ɓata Wa Rai, Ya Buƙaci Haɗin Kan APC A Katsina

LABARAI MASU NASABA

An Jikkata Mutane, An Lalata Motocin Kamfen A Taron Obi Da Kwankwaso A Delta

An Jikkata Mutane, An Lalata Motocin Kamfen A Taron Obi Da Kwankwaso A Delta

November 8, 2026
Messi Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare Ta MLS A Karo Na Biyu A Jere

Messi Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare Ta MLS A Karo Na Biyu A Jere

November 8, 2026
Hanyoyin Kare Fata Daga Illar Hasken Rana

Hanyoyin Kare Fata Daga Illar Hasken Rana

November 8, 2026
 Shin Tauraruwar Rarara Ta Fara Dusashewa?

 Shin Tauraruwar Rarara Ta Fara Dusashewa?

November 8, 2026
Jerin Sabbin Jarumai Matan Kannywood Takwas Da Za Su Ja Zarensu A 2027

Jerin Sabbin Jarumai Matan Kannywood Takwas Da Za Su Ja Zarensu A 2027

November 8, 2026
Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

Sabon Hukuncin Kotu Kan ADC Na Iya Janyo Yaƙin Basasa — Amaechi

November 8, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

Zaɓen 2027 Zai Fayyace Makomar Matasa — Tinubu

November 8, 2026
Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

November 7, 2026
Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

Shugaban Hukumar Shirin Raya Kasa Ta MDD Ya Yi Bayani Game Da Babbar Ma’anar Bikin CIIE

November 7, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Bude Kofa Mai Inganci Don Kyautata Samar Da Abinci A Duniya A Shanghai

November 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.