Mahaifiyar wani matashin da ke shirin fara NYSC, wanda masu garkuwa da mutane suka saki bayan sace shi tare da wasu, ta ce ta biya naira miliyan 6 domin a sake shi.
An yi garkuwa da matasan ne a ranar 1 ga watan Oktoba, bayan da wasu ’yan bindiga suka kai wa motocinsu ƙirar bas guda biyu da suka taso daga Ibadan ta hanyar Owerri zuwa Onitsha hari.
Mahaifiyar ta ce da farko masu garkuwar sun buƙaci naira miliyan 50 a kan kowane mutum, amma daga baya suka amince a biya naira miliyan 6 domin a saki ɗanta.
Ta ce ’yan uwanta ne suka kai kuɗin, kuma daga baya aka sako waɗanda aka yi garkuwa da su.
Ta ce lamarin ya jefa ta cikin matsananciyar damuwa, har ta kasa yin barci, amma ta samu sauƙi sosai bayan ta ji labarin cewa an sako ɗanta














