Sabbin bayanai daga hukumar kula da makamashi ta kasar Sin sun nuna cewa, zuwa karshen watan Yulin bana, lantarkin da Sin ta samar daga hasken rana ya kai kilowatt biliyan 1.286, wanda a karon farko ya zarce wanda ake samarwa daga kwal, wannan ya sa hasken rana ya zama hanya mafi girma ta samar da lantarki a kasar Sin.
Lantarkin da aka samar daga hasken rana, ya dauki kaso 31.5 na yawan lantarkin da Sin ta samar. Daga watan Janairu zuwa Yulin bana, lantarkin da Sin ta samar daga hasken rana ya zarce kilowatt-sa’a biliyan 802.4, wanda ya karu da kaso 15.5 kan mizanin shekara-shekara.
Bugu da kari, ana samar da 8 daga cikin allunan sola 10 na duniya ne a kasar Sin. Fasahar kasar Sin a wannan bangare na zaman daya daga cikin wadanda ke kan gaba a duniya, inda yanzu haka ake gaggauta nazari da samar da ingantattun fasahohin samar da lantarki daga hasken rana da za a fara amfani da su a nan gaba. (Fa’iza Mustapha)














