Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Jamus, Antonio Rüdiger, ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasar tasa kwallon kafa ta kasa da kasa.
Rüdiger, mai shekaru 33, ya sanar da matakin ne ranar Talata, watanni biyu bayan ya buga wasansa na karshe wa Jamus a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Dan wasan ya buga wasanni 86 wa Jamus, wadda ta lashe kofin duniya sau hudu.
ADVERTISEMENT
A cikin wata sanarwa da ya wallafa shafin sada zumunta, Rüdiger ya ce, “Bayan na dauki lokaci ina yin tunani, lokaci ya yi da zan kawo karshen rayuwata a tawagar kasar tare da ba wa matasa damar maye gurbina.”














