Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojin Nijeriya da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan wani jami’in soja musulmi ɗan ƙabilar Igbo, Kanar Abdur-Razaq AbdulKarim Ode, tare da gano waɗanda ke da hannu a lamarin domin a hukunta su bisa doka.
A cikin wata sanarwa da Yarima Bashir Adefaka ya fitar a madadin Tawagar Yaɗa Labarai ta Sarkin Musulmi a ranar Laraba, Sarkin ya kuma yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da yaɗa kalaman ƙiyayya da nuna wariya ga Musulman Igbo tsiraru a yankin Kudu maso Gabas, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga ƙoƙarin gina haɗin kan ƙasa.
Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ya ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya da Rundunar Soji su gano hakikanin abin da ya faru game da zargin harbe Kanar Ode har lahira a gidansa da ke Abuja.
Ya ce ya kamata gwamnati da sojoji su binciki yadda aka yi aka harbi Kanar Ode daga kusa, yana mai bayyana marigayin a matsayin “ƙwararren jami’in leƙen asirin soja” wanda ya samu girmamawa daga al’ummar Musulmi da shugabannin gargajiya, musamman a yankinsa.
Sarkin Musulmi ya jaddada cewa ba za a amince a bar kisan kowane ɗan Nijeriya ba tare da cikakken bincike da hukunta masu hannu a ciki ba, musamman idan wanda aka kashe jami’in soja ne mai yi wa Tarayyar Nijeriya hidima.














