Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya nemi wata Babbar Kotun Tarayya da ta tilasta wa jam’iyyar ADC cire sunan Ibrahim Ali Amin, wanda aka fi sani da Little, daga cikin sunayen da jam’iyyar ta mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a matsayin dan takararta na gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2027.
Sheikh Khalil ya kuma nemi kotun ta umarci ADC da ta maye gurbin sunan Amin Little da nasa.
Khalil, wanda shi ne shugaban Majalisar Malaman Kano, ya kasance cikin wadanda suka nemi zama ‘yan takarar gwamnan Kano na ADC a zaɓen 2027.
A lokacin da Musa Ungogo ke matsayin shugaban jam’iyyar ADC a jihar, jam’iyyar ta ayyana Sheikh Khalil a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar.
Sai dai bayan rushe kwamitin zartarwar jam’iyyar na jihar, ADC ta miƙa sunan Ibrahim Ali Little ga INEC a matsayin ɗan takararta. Little na da kusanci na siyasa da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Lauyan Sheikh Khalil, AA Abubakar, ya shaida wa kotun cewa an riga an kai wa dukkan waɗanda ake ƙara takardun shari’ar.
Shi ma lauyan Amin Little, wanda shi ne wanda ake ƙara na biyu a shari’ar, ya tabbatar wa kotun cewa an miƙa musu takardun shari’ar kamar yadda aka bayyana.














