ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Sin

A farkon watan Yuli, sakamakon guguwar “Maysak” da ta afku, an sami mummunar ambaliyar ruwa a yankin Guangxi da ke kudancin Sin. Gwamnatin Sin ta dauki matakan da suka dace kan lokaci, don tabbatar da kare lafiyar al’umma bisa iyakacin kokarinta. Abu mafi jawo hankali a aikin ceton a wannan karo shi ne kayan aiki masu fasahar zamani.

A cibiyar ba da ilimi na Xijiang na birnin Guigang, ruwan ambaliya ya kai zurfin kusan mita 5, inda dubban malamai da dalibai suka makale a dakunansu. Kananan jiragen ruwa da na roba suna iya daukar mutane goma ne kacal a lokaci guda, wanda ya kawo cikas ga saurin aikin ceto. A cikin wannan yanayi, wani nau’in jirgin ruwa na musamman ya ba da tallafi.Da shigarsa cikin ruwa, jirgin ruwan da aka nannade ya bude da kansa, sannan sassansa da yawa suka hade zuwa wani babban dandali a kan ruwa. Tsawonsa ya kai kusan mita 60, fadinsa kuma mita 8, yana iya daukar mutane fiye da 500 a lokaci guda. Masu aikin ceto sun yi nasarar jigilar sama da dalibai da malamai 6,000 cikin kasa da sa’o’i 24.

Masanin wata cibiyar binciken fasahar ayyukan gaggawa ta Sin Pang Linxiang ya ce, ” an sha yin amfani da wannan dandali wajen tinkarar ambaliyar ruwa a cikin kasar Sin, ya dace da lakabin da aka yi masa wato ‘jirgin ruwan ceton rai’.” Wannan batu ya bayyana yadda Sin take kokarin bunkasa kimiyya da fasaha don amfanar da jama’arta a duk fannoni.Ban da haka, a kauyen Liulan na birnin Hengzhou, ambaliyar ruwa ta lalata hanyoyi da gadoji, inda dubban mutane suka makale a cikin halin rashin ruwan sha da wutar lantarki da hanyoyin sadarwa.

ADVERTISEMENT

Masu sarrafa na’urori masu tashi sama sun isa yankin, kana tun daga safiya har zuwa dare, inda suka yi ta sarrafa na’urori masu tashi sama samfurin Q100 da suka yi jigilar ruwan sha da abinci zuwa daidai wurin da mutane suka makale.

A cikin rabin yini, an kai isashen kayan agaji zuwa kauyen da ba a iya shiga.Ba wai kawai kayan agaji ba. Yankin Zhenlong ya fuskanci matsalar katsewar sadarwa saboda bala’in. Duba da hakan, kwararrun masana fasaha goma na kamfanin sadarwa na China Mobile sun dauki na’urar samar da sigina da nauyinsa ya kai kilogiram 20, suka tafi garin Zhenlong da kafa, inda suka kafa tashar sadarwa ta tauraron dan adam.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Bayan kafa tashar, siginar 4G da WiFi sun samu a yankin da kewaye, kuma mutanen kauyen da suka makale na kwanaki da yawa, sun sami damar tuntubar iyalansu.A sama akwai na’urori masu tashi sama, a kan ruwa akwai “jirgin ruwan ceto”, kuma a kasa akwai ma’aikatan sadarwa da suka kafa tashar sadarwa.

Dukkansu sun nuna bunkasuwar karfin fasahar ceto na Sin. Amma babbar darajar fasaha ba ta kasance a bangaren “neman ci gaba” kawai ba, a’a, ya kamata ta kasance mai bautawa jama’a.

Lokacin da “jirgin ruwan ceto” ya ceto dubban dalibai, lokacin da na’urori masu tashi sama suka samar da kayan agaji, da kuma lokacin da tauraron dan adam ta sake samar da sigina, sun bayyana matsayin da Sin take dauka, wato dole ne ci gaban fasaha da kimiyya ya shafi kowane mutum, ya kuma sanya muradun jama’a a gaban komai a duk fannoni, ciki hadda lokacin da ake fuskantar bala’u.(Marubuciya: MINA)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci
  • Sulaiman
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • Sulaiman
    Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

LABARAI MASU NASABA

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.