ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

by Sani Anwar
2 months ago
Nijeriya

Babban Hafsan Sojan Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa; haɗin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula, yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa.

Shaibu ya bayyana hakan ne jiya, yayin wani taron kiwon lafiya da aka gudanar a al’ummar Okrika a Jihar Ribas, a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin ranar sojojin Nijeriya na 2026 (NADCEL).

Babban Hafsan Sojan Ƙasa, wanda kwamandan rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Emmanuel Mustapha, ya wakilta, ya ce; lafiyar al’umma na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa.

ADVERTISEMENT

“Bikin Ranar Sojojin Nijeriya, na ba mu dama ba kawai don tunawa da jarumtaka, sadaukarwa da nasarorin da jami’anmu na sojoji suka samu wajen kare ƙasarmu ba, har ma da ƙarfafa dangantakarmu da al’ummomin da muke yi wa hidima.

Wannan aikin kiwon lafiya, na nuna jajircewar sojojin Nijeriya ga sha’anin lafiya, walwala da wadatar al’ummar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“Sojojin Nijeriya sun fahimci cewa, tsaro da ci gaba suna da alaƙa ta ƙut-da-ƙut. Yawan al’umma lafiyayyu, na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa da kuma ɗorewar zaman lafiya.” “Yayin da sojojinmu ke ci gaba da fuskantar rashin tsaro a wurare daban-daban na aiki, ciki har da ta’addanci, fashi da makami, sace-sacen mai, da sauran ayyukan laifuka, muna ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa hukumomin farar hula ta hanyar shirye-shiryen agaji da na al’umma kamar haka.

“An shirya wayar da kan jama’a a yau, domin samar da shawarwari kyauta na likita, binciken ɗakin gwaje-gwaje, magani, ilimin lafiya da ayyukan tura mutane ga membobin wannan al’umma,” in ji shi.

Shugaban rundunar sojin ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, wayar da kan jama’a ta hanyar kiwon lafiya, ba wai kawai zai magance matsalolin lafiya nan take ba ne, har ma da ƙarfafa salon rayuwa mai inganci da kuma wayar da kan jama’a game da rigakafin cututtuka.

Har ila yau, ya yaba wa Ƙaramar Hukumar Okrika, sakamakon haɗin gwiwarta, kuma ya tabbatar da cewa; rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da duk masu ruwa da tsaki, don inganta zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba.

Babban Hafsan Sojan Ƙasa, ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu inganci da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’ummomi.

Nijeriya
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.