ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

by Sani Anwar
2 months ago
Ambaliyar

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet), ta yi gargaɗin cewa; jihohi 27 a faɗin ƙasar nan, za su iya fuskantar ambaliyar ruwa mai ƙarfi daga tsakanin 1 ga watan Yuli zuwa 10 ga Yuli, yayin da damina ke ƙara ƙarfi.

A cikin hasashenta na barazanar ambaliyar ruwa mai ƙarfi a cikin shekaru goma na farko na watan Yuli, hukumar ta ce; ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a watan Yuni ya bar ƙasa ta cika sosai, wanda hakan ya sa yankuna da dama suka fi fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, sakamakon ƙarin ruwan sama.

NiMet ta bayyana cewa, ƙololuwar lokacin ruwan sama, yawanci yana farawa ne a watan Yuli, wanda ke ƙara yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa, musamman a yankunan da ke da ƙarancin ruwa, birane, yankunan bakin teku da kuma wuraren da tsarin magudanar ruwansu ba shi da kyau.

ADVERTISEMENT

Jihohin da aka gano suna cikin hatsari, sun haɗa da Taraba, Sakkwato, Borno, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Nasarawa, Filato, Adamawa, Kwara, Kogi, Oyo, Ogun, Legas, Osun, Ekiti, Delta, Edo, Abiya, Imo, Anambira, Inugu, Akwa Ibom, Kuros Riba, Ribas da kuma Bayelsa.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa, ruwan sama mai tsanani zai iya kawo cikas ga ayyukan wutar lantarki da sadarwa a yankunan da abin ya shafa. Har ila yau, an shawarci masu ababen hawa da masu zirga-zirgar jiragen sama, da su yi taka-tsantsan sakamakon cewa; ruwan sama mai ƙarfi zai iya rage gani.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

NiMet ta ƙara yin gargaɗin cewa, ambaliyar ruwa na iya lalata hanyoyi, gadoji, kayayyakin more rayuwa na magudanar ruwa da filayen noma, wanda hakan ke haifar da asarar amfanin gona. Ta kuma yi kira ga hukumomin lafiya, da su shirya don yiwuwar ƙaruwar cututtukan da ke yaɗuwa, sakamakon ambaliyar ruwa da rashin tsaftar muhalli.

Ambaliyar
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara

An Kashe Fitaccen Kwamandan ’Yan Bindiga, Kachalla Sani Yellow A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.