ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago
Fim

An shafe tsawon lokaci ana tafka muhawara akan  shirin KADDARA mai dogon zango da kamfanin Abnur Entertainment ke shiryawa, yanzu dai an kammala ɗaukar fim ɗin amma kuma ya wuce ya bar wata ƙ

ullalliyar tambaya a zukatan masu kallo da har yanzu suka kasa samun amsarta, tambayar ita ce, ANYA ANA SAMUN IRIN WANNAN KADDARAR?, a cikin shirin da aka shafe watanni ana gutsurawa masu kallo, an ga wata mata mai suna Maimuna cikin wani irin yanayi na rashin dacewa a gidajenta na aure.

A auren Maimuna na farko dai ta haɗu da miji irin masu tsananin kishin da basu iya jure ganin wani ya raɓe ta ko da ace ɗan uwanta ne kuwa, har ta kai ga ya hanata amfani da wayarta ta hannu tareda buƙ

ADVERTISEMENT

atar ta goge duk wani shafi da takeda shi a kafafen sada zumunta abinda ta nuna turjiya akai, daga ƙarshe dai auren Maimuna da mijinta na farko ya mutu ba tareda an cimma wata matsaya ba.

Mijinta na biyu kuwa sai aka sameshi irin mutanen nan ne da Ibada bata damesu ba, a taƙaice dai mijin Maimuna na biyu ko Sallah ba ya yi akan lokaci, watarana ma sai ya manta da yin Sallar bakiɗaya, matar tayi iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta dawo da mijin nata ya ci gaba da kula da Ibada amma haƙarta bata cimma ruwa ba inda har yakai ga cewa matuƙar za ta matsa mashi to za su iya rabuwa, daga ƙarshe dai haka aka yi, dole auren ya mutu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Aure na uku da Maimuna tayi shine inda ta auri wani hamshaƙin mai kuɗi kuma ɗan boko inda suke zaune Lafiya ƙalau na tsawon lokaci ba kamar a sauren gidajen da ta fito ba, matsala ɗaya da ta fuskanta a auren mai kuɗin shi ne yadda mahaifiyar mijin nata taƙi ta goyi bayan zuwan Maimuna makaranta domin cigaba da karatunta, inda ta ce dole ne ta tsaya wajen kula da yayan mijin nata marayu da mahaifiyarsu ta rasu ta bari, ana haka kwatsam sai mutuwa ta ɗauke mijin nata.

Dagananan Maimuna ta sake wani auren, amma a wannan lokacin ba mai kuɗi tasamu ba, hasalima sabon angon ya daɗe yana roƙon Allah ya haɗa shi da wata mai abin hannunta ya yi wuf da ita, duba da cewar Maimuna ta samu yan kuɗaɗe bayan rasuwar mijinta na baya, sabon mijin nata ya yi amfani da wannan damar da ya samu yayi babakere da Dukiyar Maimuna, ba tare da la’akarin cewa Dukiyar ta marayu bace, almubazzarancin sabon mijin na daga cikin abinda ya janyo aurensu ya rabu da Maimuna

Harwayau dai KADDARAR da ke bibiyar Maimuna ba ta ƙare ba, domin kuwa aurenta na gaba kuma na biyar shi ne wanda ta auri wani bawan Allah wanda yake da lalurar da ta hana shi haɗa gado da sabuwar amaryar tashi, tunda Maimuna ta gano hakan sai ta fara kokwanton ɗorewar auren, daga ƙarshe dai haka ta faru dole auren ya mutu, domin kowa yaje ya samu daidai dashi.

Amma dai daga ƙarshe Maimuna ta samu salama a aurenta na gaba, inda ta auri ɗan uwanta wanda tunda farko masu kallo suka yi tunanin babu Aure a tsakaninsu sakamakon zamansu a Gida daya,wannan fim ɗin ya janyo wa waɗanda suka shirya shi da suka hada da Marubucin Labarin, Darakta da kuma Furodusa yabo daga masu kallon fim ɗin, inda suka ce wannan fim ɗin ya nuna yadda ake jaraba mutum, idan kuma yayi haƙuri daga ƙarshe sai ya ga ribar haƙurin.

Fim
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Hukumomin Kasar Sin Sun Tsara Shirin Kandagarkin Ambaliyar Ruwa

Hukumomin Kasar Sin Sun Tsara Shirin Kandagarkin Ambaliyar Ruwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.