ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Kaduna

Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta kama mutum shida da ake zargi da hannu a kisan wasu matafiya biyu da wasu fusatattun mutane suka yi a ƙauyen Gidan Kalu da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Yero ta jihar.

An bayyana sunayen waɗanda aka kashe da Muhammadu Sani, mai shekara 45, da Aliyu Mohammed, mai shekara 40, dukkaninsu mazauna ƙauyen Umar da ke Ƙaramar Hukumar Igabi. Rahotanni sun ce suna kan babur ne zuwa Tudun Wada, Zariya, domin duba wani ɗan uwansu mara lafiya lokacin da lamarin ya faru a ranar 1 ga Yuli, 2026.

A cewar ƴansanda, yayin da suke wucewa ta ƙauyen Gidan Kalu, kusa da Maraban Jos, wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa su ɓarayi ne saboda sun gan su a kan sabon babur, inda suka fara ihu da cewa, “ɓarayi ne.”

ADVERTISEMENT

Saboda tsoron kada a kai musu hari, mutanen biyu sun bar babur ɗin suka gudu. Sai dai wasu fusatattun mutane suka bi su, duk da cewa sun yi ƙoƙarin bayyana cewa ba masu laifi ba ne.

Ƴansanda sun ce har ma wasu daga cikin waɗanda suka kai harin sun san mutanen, amma duk da haka suka yi musu duka har suka mutu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Rundunar ta ce jami’anta daga Sashen Birnin Yero sun isa wurin da gaggawa bayan samun rahoton lamarin, inda suka kama Abdullahi Mukailu Kigo da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan.

A cewar rundunar, waɗanda aka kama sun amsa rawar da suka taka a lamarin, kuma suna tsare yayin da ake ci gaba da bincike domin gano da kuma cafke sauran waɗanda suka shiga harin.

Kwamishinan Ƴansandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yi Allah wadai da abin da ya faru, yana mai bayyana kisan gilla da taron jama’a ya aikata a matsayin aikin rashin ɗa’a. Ya kuma sha alwashin gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a lamarin, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

Ya gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a abin da ake kira ɗaukar doka a hannu (jungle justice) zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Kwamishinan ya tunatar da jama’a cewa kotu ce za ta tabbatar da wanda bai da laifi da mai laifi, tare da ƙarfafa su da su riƙa kai rahoton waɗanda suke zargi ga ƴansanda ko sauran hukumomin tsaro domin gudanar da bincike da bin doka.

Wannan sabon lamari ya faru ne makonni kaɗan bayan da wasu fusatattun mutane suka kashe tare da ƙona Malama Ummulkhair, malamar makarantar Islamiyya, bisa zargin sata yara wanda daga baya aka tabbatar ƙarya ce. Lamarin ya faru ne a Maraban Jos, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, a ranar 21 ga Yuni, 2026.

Rahotanni sun ce wasu mazauna yankin sun zarge ta da yunƙurin satar yara yayin da take kan hanyarta ta zuwa wani wa’azin addini a ranar Lahadi da rana.

Zargin ya bazu cikin sauri, wanda ya jawo taron jama’a suka kai mata hari kafin jami’an tsaro su ceto ta tare da kai ta ofishin ƴansanda domin kariya.

Sai dai daga baya, ɗaruruwan matasa da mazauna yankin sun kewaye ofishin ƴansandan suna neman a miƙa musu ita. Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na shawo kan lamarin, taron jama’ar ya rinjayi jami’an, ya fitar da ita tare da ƙona ta har lahira.

Daga bisani, Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 24 a gaban Kotun Majistare bisa zarginsu da hannu a kisan Malama Ummulkhair.

Kotun ta ba da umarnin a tsare dukkan waɗanda ake tuhuma a gidan gyaran hali har zuwa lokacin yanke hukunci, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 21 ga Yuli, 2026.

Kaduna
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.