ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Ƙwadago Sun Buƙaci Naira 300,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

by Sani Anwar
2 months ago
Naira

Ƙungiyar Ma’aikatan Tarayya (FWF), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan haƙƙoƙin ma’aikatan da ke wannan ƙasa, ta aiwatar da mafi ƙarancin albashi na ƙasa na naira 300,000, sannan ta magance abin da ta bayyana a matsayin mafi muni a cibiyoyin gyaran hali na ƙasar.

Mai kula da harkokin ƙungiyar na ƙasa, Mista Andrew Emelieze, ya gabatar da buƙatun a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Emelieze, ya yi kira ga gwamnati da ta biya bashin albashin watanni biyu da ke kan ma’aikatan tarayya, tun daga watan Yunin 2024, ta biya bashin kashi 40 cikin 100 na alawus na musamman, sannan ta biya dukkanin basussukan ma’aikatan tarayya, waɗanda aka aiwatar na sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa na naira 70,000.

ADVERTISEMENT

“Muna tunatar da gwamnatin tarayya nauyin da ke kanta na ma’aikatan tarayya, gami da albashin wata biyu, bashin alawus na musamman da kuma cikakken aiwatar da mafi ƙarancin albashi na 70,000,” in ji shi.

Mai kula da harkokin ƙungiyar, ya kuma buƙaci Shugaba Bola Tinubu, da ya yi gaggawar yin bitar albashin ma’aikata, yana mai jayayya cewa; albashin da ake samu a yanzu, bai isa ya maye gurbin hauhawar farashin kayayyaki ba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“Muna sake nanata shawararmu ta mafi ƙarancin albashi na 300,000 da matsakaicin albashi na naira miliyan 1.5 ga ma’aikatan da ke mataki na 17. Muna jiran amsa nan take daga Mista Shugaban Ƙasa,” in ji shi.

Bayan walwalar ma’aikata, Emelieze ya nuna damuwa kan yanayin jami’an gyaran hali, yana zargin cewa; an tilasta wa mutane da yawa sayen kayan aiki na hukuma da suka haɗa da takalma, bel, tambarin matsayi da sauran kayan aiki tare da kuɗaɗensu.

Ya kuma yi zargin cewa, jami’an da ke zaman jarrabawar ƙarin girma, sun ba da gudummawar kuɗi don jin daɗin masu jarrabawar, yana mai ƙarawa da cewa; an ruwaito cewa, irin waɗannan ayyuka sun kasance a cikin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya.

“Muna kira da a gudanar da bincike mai zurfi, kan zarge-zargen cin hanci, yayin atisayen ƙarin girma, kuma muna buƙatar inganta jin daɗin jami’an gyaran hali da sauran ma’aikatan tsaro,” in ji shi.

Naira
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
‘Lokaci Ya Yi Na Ɗaukar Mataki Kan Masu Yanke Hukunci Da Kansu’

Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.