A ranar 24 ga watan nan, shugaban kasar Serbia Aleksandar Vučić ya sauka a birnin Beijing, domin gudanar da ziyarar aiki na kwanaki biyar a kasar Sin.
Ziyarar ta kasance ta farko da shugaba Vučić ya gudanar a kasar Sin, tun bayan zamansa shugaban kasar a shekarar 2017.
A wata zantawa da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, shugaba Vučić ya sake jaddada matsayin yankin Taiwan, yana mai cewa bai fahimci manufar wasu mutane dake yunkurin tada rikici, da haifar da matsaloli kan batun Taiwan ba, duk da cewa batun ba na kasa da kasa ba ne, wato batu ne na harkokin cikin gidan kasar Sin. Ya ce bisa kundin tsarin mulkin MDD, babu shakka Taiwan yanki ne na kasar Sin. (Zainab Zhang)















Discussion about this post