Da yammacin jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun ziyarci babban gidan adana kayayyakin tarihi na kasar Masar, bisa rakiyar shugaba Abdel Fattah El-Sisi da uwargidansa Entissar El-Sisi.
Xi Jinping ya ce, a matsayin kasashe masu dadadden tarihi, kuma masu albarkatun kayayyakin tarihi a duniyarmu, ya kamata Sin da Masar su karfafa ra’ayoyin kare adalci, da koyi daga juna, da yin mu’amala, da kuma nuna fahimtar juna, domin hada kansu wajen inganta zaman daidaito a tsakanin al’adu daban daban, da yin mu’amala da koyi daga juna, ta yadda za a karfafa dunkulawar bil Adama.
A nasa bangare kuma, shugaba Abdel Fattah El-Sisi ya ce, dadadden wayewar kai na Misirawa da Sinawa yana kama da juna ta fuskar bude kofa, da hakuri da juna, da kuma zaman daidaito yayin da ake lura da bambanci, wanda hakan ya dace da shawarar wayewar kan duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Ya ce, Masar na fatan zurfafa mu’amalar jama’a, da al’adu a tsakaninta da kasar Sin, domin inganta aikin koyi daga juna tsakanin wayewar kai daban daban, ta yadda za a karfafa zaman jituwa a tsakanin kasa da kasa.
A daren jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Masar. Kana, shugaban kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi da uwargidansa sun yi ban kwana da shugaba Xi a filin jirgin sama yayin da yake kama hanya zuwa gida. (Mai Fassara: Maryam Yang)














